Wani 'Dan Fashi ya sace Motoci 32 cikin shekaru 2 a jihar Ondo
Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Ondo ta dakume wani gawurtaccen dan fashi da ya yi kaurin suna tare da shahara akn satar Motoci.
A yayin gabatar da wannan dan ta'adda, Olayemi Adeoye ga manema labarai a shelkwatar hukumar dake birnin Akure, kakakin ta Femi Joseph ya bayyana cewa, azal ce ta afka ma sa yayin da yayi yunkurin satar wata mota kirar Toyota Corolla mallakin wani mutum, Mista Olanipekun.
Hukumar ta dakume Olayemi tare da abokin sana'ar sa, Waheed Anifowose, mai facin taya da ya saba kawo masu sayen motocin da zarar an sato su.
Olayemi mai sana'ar Walda da hukumar 'yan sanda ta dakume yayin satar motar mai lamba SS719 AAA ya bayyana cewa, ya na matukar samun annashuwa da farin ciki a duk sa'ilin da yayi satar mota musamman masu amfani da dan mabudi.
Kakakin ya ci gaba da cewa, Olayemi ya shiga hannun hukumar ne inda aka sallame shi a ranar 15 ga watan Yunin da ya gabata kafin ta sake kai masa wawura a wannan lokaci.
KARANTA KUMA: Buhari zai sha kashi hannun Atiku a Zaben 2019 - PDP Adamawa
Mista Femi ya kara da cewa, akwai sa hannun Olayemi a satar Motoci 32 cikin shekarun biyun da suka gabata, sai dai yana mamakin yadda yake kubuta daga dauri kuma ya sake komawa cikin al'umma inda yake ci gaba ta tafka ta'asar sa.
Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu hukumar ta daura damara domin tabbatar da hukunta wannan shu'umin mutum tare da ci gaba da gudanar da bincike wajen bankado sauran motocin da ya yi awon gaba da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng