Aisha Bello Mustapha: Muhimmin Abubuwa 5 Dangane da Shahararriyar Ma'akaciyar NTA da Ta Rasu a Abuja
- Tsohuwar mai watsa labarai ta NTA, Aisha Bello Mustapha ta rasu kamar yadda ƴan uwanta suka tabbatar a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba
- Sai dai ba a bayyana musabbabin rasuwar ta ba amma za a yi sallar jana'izarta a babban masallacin Abuja da ƙarfe 1 na rana a ranar Litinin
- An tattaro muhimman abubuwan sani dangane da marigayiya Aisha, wacce tayi ritaya a watan Mayun 2022 bayan ta shafe shekaru 35 tana aiki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shahararriyar mai gabatar da labarai ta gidan talabijin na Najeriya (NTA), Aisha Bello Mustapha, ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a Abuja.
Mai gabatar da shirye-shiryen wacce ta kasance shahararriyar fuska ce a gidan talabijin na Najeriya a shekarun 1990 zuwa farkon 2000, ta yi ritaya daga NTA a watan Mayun 2022, in ji BBC Pidgin.
Zainab Sabo, ƙawar iyalan Aisha ta tabbatar da rasuwar inda ta ƙara da cewa za a yi sallar jana'izarta a babban masallacin Abuja da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gaskiya ne Mama (Aisha) ta rasu, kuma za’a yi sallar jana’izarta da ƙarfe 1:00 na rana. Haƙiƙa za mu yi kewarta kuma muna addu’ar Allah ya jikanta da rahama." Zainab ta shaida wa BBC Pidgin.
Bayani akan Aisha Bello Mustapha
A wannan labarin an kawo taƙaitattun bayanai kan marigayiya Aisha Bello Mustapha.
Ta yi ritaya a watan Mayun 2002
Bayan shafe shekaru 35 tana aiki da hukumar gidan talabijin ta Najeriya (NTA), Aisha ta yi ritaya a watan Mayun 2022, wanda ya kawo karshen rawar da ta taka a harkar yaɗa labarai.
Tsohuwar Babbar manaja a shirin majalisa na NTA
Marigayiya A’isha ta ƙware sosai kuma a cikin fasaharta sun haɗa da aikin jarida, shirye-shiryen talabijin, watsa shirye-shirye, tacewa, da kuma matsayinta na ƙarshe na babbar Manaja ta shirin Majalisa na NTA kafin ta yi ritaya.
Shahararriyar mai watsa labarai
Ƙwarewarta da salonta na musamman sun sanya ta zama a matsayin ɗaya daga cikin fitattun fuskoki da muryoyin NTA, wanda ya sanya ta zama abar kwatance a waje watsa shirye-shirye a Najeriya.
Aisha, tsohuwar mai watsa labarai
Tarihin da Aisha ta kafa a kafafen yaɗa labarai na Najeriya yana da girma. Ta fara aike ne a NTA, inda ta zama mataimakiyar darakta a labarai sannan ta zama babban manajan a shirin majalisa na NTA.
Marigayiyar ta kuma kasance ɗaya daga cikin fitattun masu watsa shirye-shirye a labaran sadarwa na NTA a shekarun 1990 da farkon 2000.
Ta yi digiri a ABU
A ɓangaren karatu, marigayiyar ta samu digirin farko a fannin sadarwa a jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, da ke jihar Kaduna.
Tsohon Sakataren NUPENG Ya Rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren ƙungiyar NUPENG, Frank Kokori ya riga mu gidan gaskiya.
Kokori wanda jigo ne a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya rasu yana da shekara 80 bayan ya yi fama da jinya.
Asali: Legit.ng