Yadda Mutumin Da Ke Aikin Wanke Bandaki a Turai Ya Siya Gida Daga Albashinsa, Bidiyon Ya Yadu
- Wani mutumi da ya samu rufin asiri da aikin wanke bandaki a kasar Canada ya burge mutane da dama da labarin nasararsa
- Mutumin ya bayyana cewa mutane da dama na ta yi masa ba’a saboda irin aikin da yake yi
- Masu amfani da TikTok da suka kalli bidiyon hadadden gidansa a Canada sun jinjinawa kwazonsa a kan aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani matashin mutum da ya dauki kasadar zuwa kasar Canada neman aikin yi ya cimma nasara a karshe.
Mutumin ya nunawa mutane sabon gidan da ya siya daga aikin wanke bandaki a kasar Canada.
Wani mutum ya samu aikin wanke bandaki a Canada
A cikin bidiyon, mutumin ya ce mutane da dama sun yi masa dariya da farko saboda irin aikin da yake yi ba tare da jin kunya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin (@diandersons) ya fada wa mutane cewa kada su yanke kauna da cimma mafarkinsu. Watanni da da dama da suka gabata, wannan mutumin dai ya ba da labarin yadda matarsa ta taba taimaka masa ya yi karatu a turai.
Kalli bidiyonsa a kasa:
Jama'a sun yi martani kan bidiyon
user3105710931795 ya ce:
"Aiki guda da nake jin tsoro....wanke bandakin wani daban."
Merey ta ce:
"Nagode kwanan nan na fara aikin goge-goge babu sauki da yara 4 na kan ji kamar na hakura."
Samantha ta ce:
"Na tayaka murna. Wannan shine ainahin karfafawa ga mutane da dama. Abun da yake bukata kawai shine tanadi da azama."
Henritta ta ce:
"Ina taya murna kuma cewa burin shi ne hanyar budi."
callme_neka ta ce:
"Allah da lokaci!!! ina mai sake tayaka murna!!!"
user2909099773014 ya ce:
"Na roki Allah ya mun irin budinka dan uwa. Na tayaka murna."
UCHENNA ya ce:
"Na iya wanke bandaki."
Matashiya ta kama aikin noma a turai
A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiya yar Najeriya ta ba da labarin yadda rayuwa ta kasance mata bayan ta yi balaguro daga kasar zuwa turai.
Matashiyar ta ce kafin ta bar kasar, ta siyar da gaba daya kasuwancinta (shago) sannan ta sallami ma’aikatanta.
Asali: Legit.ng