Gwamna Uba Sani Ya Ɗauki Wasu Muhimman Matakai Masu Kyau Kan Jefa Wa Musulmi Bam a Tudun Biri

Gwamna Uba Sani Ya Ɗauki Wasu Muhimman Matakai Masu Kyau Kan Jefa Wa Musulmi Bam a Tudun Biri

  • Malam Uba Sani ya ce gwamnatin Kaduna zata yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci ga al'ummar kauyen Tudun Biri
  • Gwamnan ya ce zai bi diddigin binciken da za a yi har zuwa ƙarshe domin tabbatar da an hukunta masu laifi a harin bam ɗin
  • Ya ce gwamnatin ta ɗauki nauyin kula da waɗanda suka ji raunuka kuma zata kula da marayun da iyayensu suka rasu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi alkawarin tabbatar da adalci ga wadanda harin bama-baman sojojin Najeriya ya rutsa da su a yankin Tudun Biri.

Malam Uba Sani ya kuma sha alawashin ci gaba da taimaka wa dangin waɗanda harin na ranar Lahadi ya shafa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC zai yi murabus daga kan mulki saboda rashin lafiya? Gaskiya ta bayyana da dalilai

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Kaduna: Zan Tabbatar da An Yi Wa Mutanen Tudun Biri Adalci, Gwamna Sani Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne yayin da yaje jawabi kan mummunan lamarin ya faru a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin matakan da Uba Sani ya ɗauka

Gwamna Sani ya jaddada kudirin gwamnati na bin diddigin binciken da za a yi tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya a kan lokaci.

Malam Uba Sani ya kuma amince da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Daily Trust ta rahoto Uba Sami na cewa:

"Abin da zan iya cewa a nan shi ne, mu a matsayinmu na gwamnatin jihar Kaduna za mu ci gaba da bin kadin bincike tare da tabbatar da cewa an yi komai cikin wa’adi."
“Amma a namu bangaren gwamnatin jihar Kaduna tana tallafa wa iyalai da kayan agaji da dama, mun yi hakan tun ranar farko da lamarin ya faru kuma har yanzu muna yi."

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

"Muna kula da dukkan waɗanda ke asibiti, muna biyan kuɗin maganin da ake masu. Mun ɗauki nauyin marayun da suka rasa iyayensu saboda akwai wanda baba da mama sun rasu, yaransu bakwai duk suna asibiti."
"Za mu yi iya kokarinmu wajen ganin mun kula da su, alhakin gwamnatinmu shi ne kare rayuka da dukiyoyin ƴan Kaduna. A matsayina na shugaban jiha zan yi iya kokarina don ganin an yi adalci.”

Gwamna Uba Sani Ya Caccaki Kalaman DHQ

A wani rahoton kuma Gwamnan Kaduna ya nuna rashin jin daɗinsa da kalaman hedkwatar tsaro cewa 'yan bindiga ne suka saje da mutane a kauyen Tudun Biri.

Malam Uba Sani ya ce wannan magana ba ta dace ba kuma ta nuna rashin kulawar sojoji, inda ya nemi mahukunta su janye ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262