“Dan Nan Zai Haddasa Rigima”: Bidiyon Kyakkyawan Yaro Mai Kama da Mace Ya Tsuma Zukatan Jama’a

“Dan Nan Zai Haddasa Rigima”: Bidiyon Kyakkyawan Yaro Mai Kama da Mace Ya Tsuma Zukatan Jama’a

  • Wani karamin yaro mai tsantsar kyawu ya yi fice a dandalin TikTok bayan mahaifiyarsa ta saki wani bidiyonsa
  • Allah ya albarkaci yaron da gashin kai mai tsawo, wanda ya sa shi yin kama da mace, musamman bayan a kaitsa masa shi
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama sun nuna sha'awarsu kan yaron sannan sun roki Allah ya azurta su da yaro kamar shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani kyakkyawan yaro mai kama da mace ya burge mutane bayan mahaifiyarsa ta wallafa bidiyonsa a dandalin TikTok.

Yaron na da tsantsar kyawu wanda yasa mutane da dama suka yi zaton mace ne, amma ko shakka babu namiji ne, kamar yadda aka tabbatar a wallafar.

Kara karanta wannan

"Ku daina auren talakawan mata da ba za su iya ba ku kudi ba": Daddy Freeze ya shawarci maza

Kyakkyawan yaro mai kama da mace
“Dan Nan Zai Haddasa Rigima”: Kyakkyawan Yaro Mai Kama da Mace Ya Tsuma Zukatan Jama’a Hoto: TikTok/@kenandmama1.
Asali: TikTok

Yaron na da dogon gashi kamar wata mace, kuma a cikin bidiyon, a yi matsa kitsen zane mai matukar kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyar yaron @kenandmama1, ta bayyana a taken da ta yi wa bidiyon cewa ta roki Allah ya ba ta kyakkyawan yaro kuma ya mallaka mata daya.

Ta rubuta:

"Na roki Allah ya ba ni kyakkyawan yaro, kuma sai yarona ya ce na cika maki mamana. Kwarai da gaske, ya zo da gashi mai yawa kuma ya tsani zuwa gidan aski."

Mabiyanta sun nuna sha'awar yaron sannan sun kuma ce za su so haihuwar yaro kamar shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon kyakkyawan yaron

@thehairville ta ce:

"Awwww. Yana da tsantsar kyawu. Na so wushiryan shi."

@brown ya ce:

"Namiji ne wannan? Ina fatan ba zai koma mace ba faa."

Kara karanta wannan

Shugaban Koriya ta Arewa ya zub da hawaye yayin da ya roki mata a kan su kara haihuwa, bidiyo ya bayyana

@astray ta ce:

"Me yasa yaron nan ya yi kama da ni? Ko dai dana ne wannan?"

@elchapo22 ta tambaya:

"Kina da wani abu da kike shafawa gashin kansa ne?"

@Loner ta ce:

"Ba dai kin yi gaggawan haifo dana ba? Koda yake ki dawo mun da dana kafin mu isa kotu."

@BIGBAIBEEYYY ta yi martani:

"Kaiii. Ya kamata dan nan ya zama nawa fa. Na san me nake fadi."

Budurwa ta roki direba ya kaita Amurka

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiya yar Najeriya ta bukaci wata motar bas ta kai ta Amurka yayin da ta dage cewa ita ta gaji da kasar nan.

Wani bidiyo da ke yawo a TikTok ya nuno lokacin da matashiyar ta tsayar da motar bas sannan ta bukaci a tukata zuwa Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng