“Nuna Mun Alama”: Budurwa Ta Ziyarci Kabarin Mahaifinta, Ta Nemi Ya Girgiza Bishiya, Bidiyon Ya Yadu

“Nuna Mun Alama”: Budurwa Ta Ziyarci Kabarin Mahaifinta, Ta Nemi Ya Girgiza Bishiya, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata kyakkyawar budurwa ta yada bidiyo mai tsuma zuciya na lokacin da ta ziyarci kabarin mahaifinta don ta tattauna da shi
  • A bidiyon, ta roki mahaifin nata da ya girgiza bishiya don ta tabbatar da cewar yana jin ta
  • Bidiyon ya janyo martani da dama daga jama'a da suka tuna rashi da suka yi na masoyansu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa ta tsuma zukata a TikTok bayan ta yada wani bidiyo na ziyarar da ta kai kabarin mahaifinta.

Matashiyar mai suna @Iromicc a TikTok ta isa kabarin mahaifinta da ya rasu don yin magana da shi amma bata ji amsa daga gare shi ba.

Budurwa ta ziyarci kabarin mahaifinta
“Nuna Mun Alama”: Budurwa Ta Ziyarci Kabarin Mahaifinta, Ta Nemi Ya Girgiza Bishiya, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @ironiccc/TikTok.
Asali: TikTok

Budurwa ta roki mahaifinta da ya rasu a kan ya girgiza bishiya

Kara karanta wannan

Yadda yaran turawa da mahaifinsu suka sharbi kuka a filin jirgi kan rabuwa da mai aikinsu

A cikin bidiyo da ya yadu, ta roke shi da ya girgiza bishiya ko wani abu domin ta tabbatar da cewar yana sauraronta, amma babu abun da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanye da bakaken kaya kuma zaune a kusa da kabarin, tana ta magana da mahaifin nata da ya mutu tare da fatan zai amsa mata.

Sai dai kuma, ta rufe hoton mahaifin nata bayan bata samu kowani alama da ke nuna yana jin ta ba.

Da ta wallafa bidiyon a TikTok ta rubuta:

"Lokacin da na zo na zauna a kabarin mahaifina don zantawa da shi sannan na fada masa ya girgiza bishiya ko wani abu don na san yana ji na amma bai yi komai ba."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Bidiyon ya haifar da martani da dama daga mutanen da suka rasa masoyansu sannan suke ji ina ma ace za su zantawa da su.

Kara karanta wannan

"Ina son mahaifinsa idan yana raye don Allah": Matashiya ta fadi dalilinta na auren tsoho

@Victoria ta ce:

"Na bukaci mahaifina da ya nuna mun alama sannan ya fara girgiza mani gadona tun daga lokacin ban sake neman wani ba bayan wannan ya tsorata ni har na kusa shidewa."

@Myjah ta yi martani:

"Ni da mahaifiyata hura mani iska ko wani abu."

@Kara ta ce:

"Shakka babu yana iya jin ki yana jin dadi idan kika yi hirar aikinki da shi."

Turawa sun yi kukan rabuwa da mai aiki

A wani labari na daban, wani bidiyo da ya yadu da yaran turawa suna sharban kuka a filin jirgin sama yayin da mai aikinsu zata tafi ya tsuma zukata a soshiyal midiya.

Mai aikin wacce ta kasance bakar fata da aka ambata da suna Rosie, ta rigada ta yi nisa lokacin da yaran wanda ya dauketa aiki suna ruga wajenta, inda suka ki bari ta tafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng