NDLEA Ta Gano Katafaren Gonar Da Ake Noman Wiwi a Sokoto, Ta Cafke Mutum Daya
Jihar Sokoto - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, shiyyar Jihar Sokoto, ranar Juma'a, ta kama wani Anas Sani, mai shekaru 32, wanda aka gano yana noman tabar wiwi a jihar.
Babban Kwamandan Hukumar a jihar, Iro Adamu, a bayaninsa, ya ce sun gano haka ne a binciken da aka gudanar daren Juma'ar da ta gabata a yankin Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar, bayan samun bayanan sirri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An shuka tabar ne a gonar masara ta yadda iya kwararru ne kawai za su iya gane menene.
"Ta waje ce mai karfi kuma mai tsada," in ji shi.
Adamu ya ce wannan ne karon farko da aka samu irin gonar a jihar, wanda ya ce, dole a gudanar da gangamin yawan wayar da kai don dakike al'umma daga fadawa haramtattun kasuwanci.
Wanda ake zargin, mai 'ya'ya biyu, da yake zantawa da manema labarai, ya ce ya koyi kasuwancin a Jihar Lagos lokacin da ya ke sana'ar kanti.
"Wannan ne karo na farko. Na koya lokacin ina rayuwa a Lagos sai na yanke shawarar yi a garinmu Sayinna.
"Babban yayana yayi bakin kokari kar na yi amma banji shawara ba.
"Nagode Allah da aka kama ni kafin in fara cin riba.
"A shirye nake na karbi hukuncin abin da na aikata saboda ya zama izna ga masu sha'awa nan gaba," in ji shi
Asali: Legit.ng