An Shiga Jimami Yayin da Mahaifiyar Tsohon Ministan Buhari Ta Rasu
- Tsohon ministan wasanni a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Solomon Dalung ya yi babban rashi
- Tsohon ministan ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa wacce ta yi bankwana da duniya tana da shekara 90
- Dalung a wani saƙo ɗa ya sanya a Facebook ya bayyana cewa mahaifyar ta sa, Ysj Chirram, ta rasu ne a safiyar ranar Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Solomon Dalong, tsohon ministan wasanni a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi alhinin rasuwar mahaifiyarsa, yana mai cewa yana cikin “lokacin baƙin ciki”.
Tsohon ministan ya bayyana rasuwar mahaifiyar ta sa ne shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.
A cewar tsohon ministan, mahaifiyar ta sa, Yah Chirram ta rasu ne tana da shekara 90 bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya a safiyar ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalung ya yi jimamin rasuwar mahaifiyarsa
Da yake sanar da rasuwar mahaifiyar ta sa, Dalung ya rubuta cewa:
"Cikin zafin zuciya na ke sanar da rasuwar mahaifiyata kuma masoyiyata. Rasuwarta ta bar wani babban giɓi, kuma na gode da ta'aziyyar da aka yi a wannan lokaci mai wahala."
"Mama ba mahaifiyata ba ce kawai, ta kasance mutum mai ban mamaki wacce kuzarinta da kwarjininta suka taɓa rayuwar mutane da yawa. Rasa mahaifiya abu ne mai wuyar gaske, kuma kyawawan abubuwan tunawa da muka yi tare zasu samu wuri na musamman a cikin zuciyata har abada."
"Ina so in nuna godiya ta game alhininku da addu'o'in ku. Taimakon ku yana nufin duniya a gare ni yayin da nake cigaba da tafiya cikin wannan lokacin baƙin ciki. Ina neman fahimtar ku yayin da nake ɗaukar lokacin da ake buƙata domin yin baƙin ciki da samun ƙarfi a cikin kyawawan tunanin rayuwar da muka yi tare da Mama.
"Ina ba ku tabbacin cewa ina sane da kyautatawarku, kuma ina godiya da haɗin kai da aka nuna a wannan tafiya mai wahala. Mu karrama Mama ta hanyar tunowa da soyayyar da ta yi mana."
Dan Majalisa Ya Rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓun Issa/Sabon Birni, Abdulkadir Jelani Danbuga ya riga mu gidan gaskiya.
Ɗan majalisar ya yi bankwana da duniya ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng