“Wannan Sheki Ne Ko Bilicin?” Sauyawar Launin Fatar Budurwa Ya Jefa Mutane a Rudu, Bidiyon Ya Yadu

“Wannan Sheki Ne Ko Bilicin?” Sauyawar Launin Fatar Budurwa Ya Jefa Mutane a Rudu, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin sauyawar launin fatarta mai ban mamaki
  • Yayin da wasu masu kallo suke ganin sheki ta kara, wasu sun ce akwai yiwuwar bilicin ta yi
  • Masu amfani da TikTok sun yi zazzafan muhawara a sashin sharhi kan yanayin sauyawarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta yi fice a dandalin TikTok bayan ta baje kolin sauyawarta cikin yan shekaru kadan.

Wata yar TikTok mai suna @orientalglitters ta baje kolin sauyawar launin fatarta, daga baka zuwa yar fara tas.

Sauyawar fatar jikin budurwa ya ba da mamaki
“Wannan Sheki Ne Ko Bilicin?” Sauyawar Fatar Wata Budurwa Ya Jefa Mutane a Rudani, Hotunan Sun Yadu Hoto: @orientalglitters/TikTok.
Asali: TikTok

Sauyawar launin fatar budurwa ya haddasa muhawara

Sauyawar fatar tata ya bar masu kallo da dama cikin mamaki da son sanin dabarun da ta yi amfani da su wajen cimma irin wannan gagarumin sauyi.

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da take nunawa duniya sauyawar tata, matashiyar ta yi yar tambaya, tana tambayar masu kallo ko ta cimma sakamakon ne ta hanyar sheki da hutu ko bilicin.

Da aka tambayeta game da yadda ta cimma wannan launi nata, matashiyar ta yi ikirarin cewa ita kwararriyar mai gyaran fata ce wacce ke hada mayuka da kanta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan sauyawar launin fatarta

Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu inda wasu suka jinjinawa sauyawarta a matsayin hutu da sheki wasu kuma sun ce bilicin ta yi.

Wadanda suka alakanta shi da bilicin sun bayyana tarin hatsarin da ke tattare da irin wannan abu.

@Vanessa Zane ta ce:

"Sheki da walwali ne bilicin za ta kasance da bakin hannu."

@pretty_damsel ta yi martani:

"Ya danganta fa. Idan ke talaka ce bilicin ne idan kuma kina da kudi sheki ne."

Kara karanta wannan

Tsige Abba Gida Gida: An kama mutum 7 kan hukuncin Kotun Daukaka Kara, cikakken bayani

@kismah ta ce:

"Bilicin ne."

@Julia ta yi martani:

"Bilicin ajin farko."

@ebyshine ta ce:

"Ba bilicin bane sheki ne."

@J ta yi martani:

"Sheki da dan bilicin saboda dai dama chan ba baka bace."

Mutum-mutumi mai kula da kwastamomi

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa an gano wata mutum-mutumi mai hikima wacce ke aiki a matsayin mai kula da kwastamomi a wani gidan cin abinci.

A wani bidiyo da ya yadu wanda @user8618773353018 ya wallafa, mutum-mutumin ta yi shiga kamar wata mace sanye da riga da wando harda takalmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng