Mulki Ya Zo Karshe: Gwamna Bello Ya Dauki Mataki, Ya Rufe Dukkan Asusun Gwamnati a Jiharsa

Mulki Ya Zo Karshe: Gwamna Bello Ya Dauki Mataki, Ya Rufe Dukkan Asusun Gwamnati a Jiharsa

  • Gwamna Yahaya Bello ya umarci a gaggauta rufe dukkan wani asusu na gwamnatin jiha da na kananan hukumomin jihar Kogi
  • Kwamishinan kuɗi na jihar, Asiwaju Asiru Idris ne ya bayyana haka, ya ce an kuma umarci dakatar da dukkan wasu hada-hadar kuɗi a asusun
  • Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Bello ke shirye-shirye sauka daga mulki bayan wa'adinsa ya ƙare a watan Janairu, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ba da umarnin a kulle dukkan asusun gwamnatin jiha da na kananan hukumomi nan take ba tare da ɓa ta lokaci ba.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Gwamma Yahaya Bello Ya Garkame Lalitar Gwamnan jihar Kogi Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

Kwamishinan kuɗi na jihar Kogi, Asiwaju Asiru Idris, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara da sanya ranar yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan Kaduna

A sanarwan da kwamishinan ya fitar yau 23 ga watan Nuwamba, 2023, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daga yanzu babu wanda za a sake biya wasu kudi ko fitar kuɗi daga lalitar gwamnati. An soke duk wani umarnin sakin kuɗi da ba a aiwatar ba ko na zuba hannun jari."
"An rufe dukkan asusun gwamnatin jihar Kogi da na ƙananan hukumomin jihar daga yau Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023."

Channels tv ta tattaro cewa wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Yahaya Bello ya caccaki muƙarrabansa bisa abin da ya kira saba wa manufofin gwamnatinsa.

Yahaya Bello ya kusa sauka daga gadon mulki

Gwamna Bello, wanda wa'adinsa a zango na biyu ke dab da karewa, ana tsammanin zai mika mulki ga zababben gwamna, Usman Ododo, a watan Janairu, 2024.

Ododo, tsohon Audita Janar na kananan hukumomi a jihar Kogi karƙashin gwamnatin Bello, kuma ɗan takarar APC, shi ne ya lashe zaɓen gwamna ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ɗau zafi, ya dakatar da kwamishina da wani babban hadimi kan abu 1 tak

Gwamna Uzodinma ya dakatar da muƙarrabansa biyu

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Imo ya dakatar da kwamishinan filaye, bincike da tsare-tsare, Honorabul Noble Atulegwu, daga muƙaminsa nan take.

Ya kuma dakatar da mai ba gwamna shawara kuma babban manajan hukumar gidaje ta jihar, Mbakwe Obi Jnr, ya umarci su bar ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262