Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Ziyarar Aiki da Ya Kai Kasar Jamus

Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Ziyarar Aiki da Ya Kai Kasar Jamus

  • Shugaba Tinubu wanda ya bar Najeriya a ranar 18 ga watan Nuwamba, don halartan taron G20 a kasar Jamus, ya dawo kasar a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba
  • A halin da ake ciki, Tinubu ya halarci taron duniya wanda ke ba shugabanni damar tattauna dabarun bunkasa hannun jari a manyan sassa don ci gaban tattalin arziki
  • Tinubu, tare da tawagar Najeriya sun taka rawar gani wajen tattaunawa da shugabannin duniya don inganta hadin gwiwar kasa da kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya iso babban birnin tarayya Abuja daga Berlin, kasar Jamus a daren Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya
Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Ziyarar Aiki da Ya Kai Kasar Jamus Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar da ya kai Jamus

Kara karanta wannan

Har yanzu Shugaba Tinubu na jinyar tiyatar da aka aasa a gwiwa, in ji Onanuga

Shugaban kasar ya dawo gida Najeriya bayan ya samu nasarar halartan taron G20 da kasashen Africa (CwA).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu, wanda ya bar Najeriya a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2023, ya isa Abuja a daren ranar Laraba, Channels TV ta rahoto.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Tinubu ya samu tarba daga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

An tarbi Tinubu ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

A yayin taron, Tinubu ya shiga sahun shugabannin kasashe, gwamnatoci, da kungiyoyin kasa da kasa, don tattauna matakan inganta hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci, tare da mai da hankali kan muhimman bangarori kamar makamashi, kasuwanci, kayayyakin more rayuwa, da sabbin fasahohi.

Kara karanta wannan

Bayan zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fadi burin da ya rage masa a Duniya

Gwamnatin Jamus da kungiyoyin yan kasuwa nesuka shirya taron na G20 da CwA da nufin karfafa dangantakar tattalin arziki da inganta zuba jari a tsakanin kasashe CwA.

Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da Jamus kan samar da iskar gas da ayyukan sabunta makamashi.

Yarjejeniyar dai na bukatar Najeriya ta samar da iskar gas ga kasar Jamus sai kuma dayan aikin makamashi na dala miliyan 500 a Najeriya.

Tinubu ya fadi abun da ya rage masa

A wani labarin, mai girma Bola Ahmed Tinubu yana da sauran buri duk da ya samu abin da yake nema na zama shugaban kasar Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu ya ce ya kamata sunan shi ya shiga cikin littafin Guinness wanda ake tattara sunayen gwarza a fagagen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng