Ana Zanga-Zanga a Kano Kan Tsige Abba Gida Gida, Bidiyo Ya Bayyana
- Zanga-zanga ta barke a jihar Kano bayan tsige Gwamna Abba Yusuf da kotun daukaka kara ta yi
- Hakan ya kasance ne yayin da yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar a yankin Dan Agundi da ke jihar a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba
- Zanga-zangar ta biyo bayan sakin kwafin shari'ar CTC wacce ta sha bamban da hukuncin kotun daukaka kara
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Magoya bayan jam'iyyar NNPP sun mamaye titunan jihar Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, domin yin zanga-zanga kan kayen da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha a kotun daukaka kara.
Daga bisani jami’an yan sandan Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba barkonon tsohuwa.
APC vs NNPP: Zanga-zanga ya barke a Kano
Jaridar Daily Trust da Channels TV ma sun fitar da rahotanni kan zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zangar ta biyo bayan sakin kwafin shari'ar CTC wacce ta sha bamban da hukuncin kotun daukaka kara.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce a shirye suke su mutu yayin da suke neman adalci.
Ga bidiyon zanga-zangar a kasa:
Kotu ta saki takardun hukuncin shari'ar Kano
A baya mun ji cewa kwanaki biyar bayan yanke hukunci, kotun daukaka ƙara ta saki takardun hukuncin shari'ar gwamnan Kano da ta yanke.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke hukuncin ne a kan zaɓen gwamnan jihar Kano da ake takaddama a kai a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, inda ta ba jam'iyyar APC da ɗan takararta, Nasiru Gawuna, nasara.
Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu, ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyar PRP a zaɓen 2023 ne ya sanya takardun na CTC a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
NNPP ta magantu kan shari'ar Kano
A gefe guda, jami'yyar NNPP ta yi martani kan rikita-rikitar da ke cikin hukuncin kotun daukaka a zaben gwamnan Kano.
Idan ba a manta ba a jiya Talata aka saki kwafin shari'ar ta CTC wacce ta sha bamban da hukuncin kotun daukaka kara, cewar Punch.
Asali: Legit.ng