Kungiyar Ma'aikatan Shari'a JUSUN Reshen Jihar Osun Ta Ayyana Shiga Yajin Aiki
- Kungiyar ma'aikatan shari'a JUSUN reshen jihar Osun ta ayyyana shiga yajin aikin sai baba ta gani ranar Laraba
- Ta ce ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan cin mutunci da harba barkonon tsohuwa da yan sanda suka yi kan mambobinta
- Shugaban ƙungiyar ya ce ba gudu ba ja da baya har sai shugabar alƙalan Osun ta amsa tambayoyin da suka aika mata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Kungiyar ma'aikatan shari'a ta Najeriya (JUSUN) reshen jihar Osun ta ayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, 2023.
Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, ƙungiyar JUSUN ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon barkonon tsohuwar da yan sanda suka harba wa mambobinta.
Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda rigima ta shiga tsakanin ma'aikatan shari'a da suka fito zanga-zanga da yan sanda a kofar shiga babbar kotun jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin dai ya kai ga jami'an yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwa mai sa hawaye saboda azaba domin tarwatsa masu zanga-zangar.
JUSUN ta tsunduma yajin aiki a Osun
Shugaban ƙungiyar JUSUN na jihar, Oluwagbemiga Eludire, shi ne ya ayyana shiga yajin aikin ma'aikatan shari'a na Osun har sai baba ta gani.
Ya bayyana cewa hakan ya zama tilas a kansu domin kawo karshen sama da faɗi da kuɗin ma'aikatan shari'a ta jihar.
Mista Eludire ya ce shugabar alkalan Osun (CJ), Mai shari’a Adepele Ojo, ta sa allura ta tono garma domin alamu sun nuna ta ɗauri ɗamarar yaƙi da ma'aikatan.
Ya ƙara da cewa kungiyar ba za ta ja da baya ba har sai ta samu gamsassun amsoshi game da tambayoyin da ta aike wa CJ wadda ke cikin tsaka mai wuya.
A rahoton jaridar Vangaurd, shugaban JUSUN ya ce:
“An dakatar da horar da ma’aikatan shari’a a NJI duk da isasshen tanadi, ga kuma rashin biyan alawus alawus na tufafi ga ma’aikatan shari’a duk da an ware kuɗin a cikin kasafin kudi."
Kotun daukaka kara zata yanke hukunci kan zaben gwamnan Nasarawa
A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta tsaida ranar yanke hukunci kan sahihin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa.
Gwamna Abdullahi Sule na APC ne ya ɗaukaka kara bayan kotun zaɓe ta tsige shi, ta ce ɗan takarar PDP ne zababben gwamna.
Asali: Legit.ng