Rigima Ta Kaure Tsakanin Yan Sanda da Ma'aikatan a Babbar Kotun Jihar PDP Kan Abu 1 Tal

Rigima Ta Kaure Tsakanin Yan Sanda da Ma'aikatan a Babbar Kotun Jihar PDP Kan Abu 1 Tal

  • Rigima ta ɓalle tsakanin yan sanda da ma'aikatan shari'a na jihar Osun a kofar shiga babbar kotu ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba
  • Rahotanni sun bayyana cewa ma'aikatan sun yi kokarin fitar da shugabar alƙalan jihar daga ofis da ƙarfin tsiya amma yan sanda suka turje
  • Ma'aikatan sun ci gaba da zanga-zanga ranar Laraba bisa zargin mai shari'a Ojo da girman kai da kuma riƙe musu haƙƙokinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - An yi arangama tsakanin dakarun rundunar ƴan sanda da kuma ma'aikatan ɓangaren shari'a a ƙofar shiga babbar kotun jihar Osun.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wannan lamari ya faru ne ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, 2023 kan shugabar alkalan jihar, mai shari'a Oyebola Ojo.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kungiyar ma'aikata JUSUN sun ayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani, bayanai sun fito

Rikici ya balle tsakanin ma'aikata da yan sanda a Osun.
Yan Sanda da Ma'aikatan Shari'a Sun Yi Arangama a Babbar Kotun Jihar Osun Hoto: thenationonline
Asali: UGC

A yau Laraba aka wayi gari ma'aikatan shari'a a jihar Osun sun ci gaba da zanga-zangar adawa da shugabar alƙalan wace kujerarta ke tangal-tangal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna ma'aikatan sun fara wannan zanga-zanga ne kan zargin Ojo da nuna girman kai da kuma riƙe masu alawus-alawus ɗinsu.

Yan sanda da ma'aikatan sun ye arangama ne yayin da tashe-tashen hankula ke kara ta'azzara kan batutuwan da suka shafi mai shari'a Ojo.

Rigimar ta ƙara tsananta ne yayin da aka ga shugabar alƙalan ta shiga Ofis, lamarin da shugabannin ƙungiyar ma'aikatan shari'a na jihar suka yi fatali da shi.

Yadda rigima ta shiga tsakanin yan sanda da ma'aikatan

An ce ma'aikatan masu zanga-zanga sun yi yunƙurin cin mutuncinta da kuma fitar da ita daga ofis da ƙarfin tsiya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Ɗaya daga cikin ɗalibai mata na jami'ar tarayya da yan bindiga suka sace ta kuɓuta

Sai dai jami’an tsaron da ke ba shugabar alkalan kariya suka hana, bisa haka suka harba barkonon tsohuwa kan ma’aikatan da suka yi yunkurin far mata.

Ma’aikatan shari’a karkashin shugaban kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) reshen jihar Osun, Kwamared Gbenga Eludire sun kutsa ofishin don fito da CJ da karfin tsiya amma ƴan sanda suka hana.

Yan sanda sun ceto ɗalibar FUDMA

A wani rahoton na daban Dakarun yan sanda sun samu nasarar ceto ɗaya daga cikin ɗalibai mata 5 da yan bindiga suka sace a jami'ar tarayya ta Dutsinma.

Mai magana da yawun yan sandan Katsina, SP Abubakar Aliyu, ya ce a halin yanzun an kai ta asibiti domin duba lafiyarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262