Babbar Kotu Ta Amince da Buƙatar Tsohon Gwamnan CBN Kan N300m, Ta Gindaya Sharudda Masu Tsauri
- Babbar kotun birnin tarayya Abuja, ranar Laraba, ta bada belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan kuɗi N300m
- Alkalin kotun mai shari'a Hamza Mu'azu ya kwace takardun tafiye-tafiyen Emefiele, ya kuma gindaya masa sharuɗɗa masu tssauri
- Wannan na zuwa ne watanni bayan wata babbar kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta amince ta ba da belin tsohon gwamnan kan N20m
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta amince da buƙatar ba da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele.
Jaridar The Cable ta tattaro cewa kotun ta bada belin tsohon gwamnan na CBN kan kuɗi Naira miliyan 300.
Bayan sauka mulki, Muhammadu Buhari ya faɗi manufa 1 tal da ta sa ya canza takardun naira a Najeriya
Wane sharuɗɗa kotu ta gindaya masa?
Daga cikin sharuɗɗan belin a cewar akalin kotun, ya zama tilas Mista Emefiele ya kawo waɗanda zasu tsaya masa mutum biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma ya zama wajibi waɗanda zasu tsaya wa tsohon gwamnan CBN ɗin su kasance suna da shaidar mallakar kadarori a cikin Maitama da ke birnin Abuja.
Kotun ta kuma wajabta wa Mista Emefiele ya miƙa dukkan takardunsa na tafiye-tafiye ga rijistaran kotun kuma ko an sake shi a beli dole ya zauna a yankin ƙaramar hukumar Abuja Municipal.
Ana tsammanin zai ci gaɓa da zama a gidan gyaran halin Kuje gabanin cika waɗannan shruɗɗan benin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne watanni hudu bayan da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da belin Emefiele kan kudi naira miliyan 20.
Mista Emefiele na fama da tuhume-tuhume a gaban ƙuliya tun bayan dakatar da shi daga matsayin gwamnan babban banki CBN.
Buhari ya bayyana dalilin canza takardun kuɗi
A wani rahoton na daban Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi bayanin manufar sake fasalin Naira da gwamnatinsa ta aiwatar ana dab da zaɓe.
Ya kuma ce gwamnatinsa ta samu nasara gagara misali a ɓangarorin tsaro da kuma tattalin arzikin ƙasa.
Asali: Legit.ng