Gwamnan PDP Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Tsige CJ, Ya Aike da Wasiƙa Ga Shugaban Alkalai Na Ƙasa

Gwamnan PDP Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Tsige CJ, Ya Aike da Wasiƙa Ga Shugaban Alkalai Na Ƙasa

  • Gwamnan jihar Osun ya canza shawara kan tsige shugaban alkalan jihar da kuma naɗa wanda zai maye gurbinsa
  • Adeleke ya rubuta wasika ya aike wa Alkalin alkalan Najeriya (CJN) kan matsayar majalisar dokokin jihar Osun
  • Idan baku manta ba, Adeleke ya naɗa mai shari'a Olayinka David Afolabi a matsayin mukaddashin CJ

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya yi amai ya lashe kan naɗa mai shari'a David Afolabi a matsayin muƙaddashin shugaban alkalan jihar.

Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya canza shawara.
Gwamna Adeleke ya yi amai ya lashe kan nadin sabon Alkalin Alkalan Osun Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Gwamnan ya naɗa sabon CJ ne domin maye gurbin tsohon shugaban alƙalan Osun mai shari'a Adepele Ojo, wanda ya tsige daga kan muƙamin.

Sai dai cece-kuce ya ɓarke a jihar bayan umarnin da majalisar dokokin Osun ta bai wa tsohon shugaban alƙalan cewa ya sauka daga kan muƙamin kan zargin rashin ɗa'a.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya dora alhakin tsige Gwamna Abba Kabir kan Kwankwaso, ya bayyana dalilansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan umarni ne ya tilastawa Gwamna Adeleke na jam'iyyar PDP naɗa mai shari'a Olayinka a matsayin shugaban alkalai na riƙo (CJ), kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Amma ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) da masu ruwa da tsaki a fannin shari'a sun yi fatali da matakin da Gwamna Adeleke da majalisar dokokin jihar Osun suka ɗauka.

Adeleke ya canza tunani, ya tura sako ga CJN

A wata sanarwa ranar Lahadi ta hannun kwamishinan yaɗa labarai na Osun, Adeleke ya ce ya tura matsaya da shawarwarin majalisar dokoki zuwa ga shugaban alkalai na kasa (CJN).

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, sanarwan ta ce:

"Gwamna Adeleke ya san cewa alkalin alƙalai na ƙasa ne shugaban majalisar shari'a ta ƙasa (NJC) kuma ya rubuta masa takarda kan matsayar da majalisa ta ɗauka bayan ƙorafe-korafe sun yi yawa kan shugaban alkalan Osun."

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

"A takardar ya faɗa wa CJN shawarar da majalisar dokoki ta yanke cewa shugaban alƙalan ya yi murabus a naɗa sabo kafin NJC ta gama nazari ta yanke hukunci kan korafe-ƙorafen."
"Daga ƙarshe, a cikin wannan takarda gwamna Adeleke ya ba CJN shawarin naɗa babban alƙali, mai shari'a Olayinka David Afolabi ta hanyar bin matakan da ya dace."

Matawalle na dab da kwace mulkin Zamfara

A wani rahoton kuma Mataimakin shuugaban APC ya yi ikirarin cewa nan ba da daɗewa ba, Bello Matawalle, zai ƙwace kujerar gwamnan Zamfara

Garba Muhammad Datti ya faɗi haka ne yayin martani kan hukuncin kotun ɗaukaka kara na soke nasarar Dauda Lawal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel