Miyagu Sun Shiga Har Cikin Ɗaki, Sun Halaka Ɗalibar HND Ta Hanya Mai Ban Tausayi a Jihar Arewa
- Wasu tsageru sun je har ɗakin wajen makaranta sun shaƙe wata ɗalibar kwalejin fasahata ta Offa a Kwara har lahira ranar Alhamis
- Hukumar makarantar ta tabbatar da kisan, inda ta ce hukumomin tsaro sun fara bincike don zaƙulo masu hannu a lamarin
- Haka nan kuma kwalejin ta tura sakon ta'aziyya ga iyalan ɗalibar, abokanta da kuma sashin koyar da fasahar abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Wasu miyagu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun halaka ɗalibar babbar diploma ta ƙasa (HND) a Kwalejin Fasaha ta tarayya, Offa a jihar Kwara.
Ɗalibar mai suna, Toyin Bamidele, wadda ke karatu a sashin koyon fasahar abinci, makasan sun shaƙe ta har lahira ranar Alhamis a gidan hayar da take zaune a wajen makaranta
Tashin hankali: Halin da mutane suka shiga a jihar Kano bayan kotun ɗaukaka ƙara Ta tsige Abba Gida-Gida
Muƙaddashin kakakin kwalejin fasahar Offa, Misis Folake Oyinloye, ta tabbatar da kashe ɗalibar ga jaridar Punch ranar Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki aka ɗauka a yanzu?
Misis Oyinloye ta bayyana cewa hukumar makaranta ta fara gudanar da bincike kan wannan kisan tare da haɗin guiwar hukumomin tsaro.
A kalamanta ta ce:
"Hukumar makaranta ta yi Allah wadai da wannan ta’asa da kakkausar murya, domin sabon abu ne faruwar irin haka a kwalejin."
"Yayin da har yanzu ba a san maƙasudin aikata wannan ɗanyen aiki ba, mun fara bincike tare da hukumomin tsaro domin zaƙulo masu hannu a kan lamarin."
"Mutuwar ɗalibar babban rashi ne ga makaranta da gaba ɗaya ma'aikatanta. Kwaleji na miƙa ta'aziyya ga dangin ɗalibar, abokai, da sashin koyar da fasahar abinci bisa wannan rashi."
Ta kuma yi kira ga duk wanda ke da bayanan da za su taimaka a binciken da ake yi su faɗa wa hukumomin tsaro domin doka ta yi aikinta, Daily Post ta ruwaito.
Duk kokarin jin ta bakin hukumar ‘yan sandan jihar Kwara ya ci tura, domin ba a samu jin ta bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Victor Olaiya, ta wayar tarho ba.
Shugaba Tinubu Ya Roƙi Yan Najeriya Muhimmin Abu 1
A wani rahoton na daban kuma Bola Ahmed Tinubu ya roƙi dukkan yan Najeriya su ba shi haɗin a kokarin yaƙi da ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Shugaban ƙasar ya nemi wannan alfarma ne yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng