Majalisar Dokokin Jigawa Ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 Saboda Laifi 1 Tak

Majalisar Dokokin Jigawa Ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 Saboda Laifi 1 Tak

  • Majalisar dokokin jihar Jigawa ta hukunta wasu shugabannin kananan hukumomi uku
  • Matakin ya biyo bayan take umurnin majalisar da ciyamomin suka yi, inda suka fita kasar waje ba tare da izini ba
  • Shugabannin kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da na Hon Mubarak Ahmed na Birniwa, Hon Rufai Sunusi na Gumel da d Hon Umar Baffa na Yankwashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Jigawa - Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku, kan zargin fita wajen kasar ba tare da sun nemi izini daga bangaren zartarwa ko na dokokin jihar ba.

Shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar sun hada da Hon Mubarak Ahmed na karamar hukumar Birniwa, Hon Rufai Sunusi na karamar hukumar Gumel da Hon Umar Baffa na karamar hukumar Yankwashi.

Majalisar Jigawa ta hukunta shugabannin kananan hukumomi 3
Majalisar Dokokin Jigawa Ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 Saboda Laifi 1 Tak Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, an yi zargin cewa yan siyasar sun lula kasar Rwanda ne.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarin gwaramar da shugabannin da suka gabacesa suka bar wa gwamnatinsa

Majalisa ta kaddamar da bincike kan shugabannin kananan hukumomin 3

Majalisar ta dauki matakin ne, bayan shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi, Hon Aminu Zakari Tsubut, ya gabatar da kudirin don dakatar da ciyamomin da abun ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa, kafin tafiyar tasu, majalisar ta bayar da wani umurni ga shugabannin kananan hukumomi a jihar na kada su yi tafiya zuwa ko'ina saboda shirya kasafin kudin jihar na 2024 da gabatar da shi gaban majalisa da gwamnan jihar, Malam Umar Namadi zai yi.

Tsubut ya bayyana matakin da shugabanin kananan hukumomin suka dauka a matsayin rashin biyayya, nuna halin ko-in-kula ga babban nauyi dake kansu wanda ya kamata a bincika tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Mamba mai wakiltar mazabar Malam Madori, Hon Usman Abdullahi Tura da mamba mai wakiltar Guri, Hon Hamza Guri sun goyi bayan kudirin da Hon Tsubut ya gabatar, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gano gaskiya, ya umarci wasu ma'aikatan Gwamnati su yi murabus

Daga nan ne majalisar ta amince da dakatarwar da aka yi wa shugabannin kananan hukumomin uku tare da umurtar mataimakan su da su karbi ragamar aiki.

Sai dai majalisar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye, Hon Lawan Muhammad Dansure don ya binciki lamarin, sannan ya mika rahotonsa ga majalisar nan da makonni hudu domin daukar mataki na gaba.

Gwamnan Jigawa ya ba mace babban mukami

A wani labarin, mun ji a baya cewa gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nada Zainab Shuaibu Rabo Ringim a matsayin babbar mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yaɗa labarai tare da wasu mataimaka 116.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar (SSG), Mallam Bala Ibrahim, cewar rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng