Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Ministan Buhari a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Ministan Buhari a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa tsohon ministan kuɗin Najeriya, Dakta Onaolapo Soleye, rasuwa yana da shekaru 90 a duniya
  • A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun bayyana cewa ya mutu ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023
  • Sun kuma yi bayanin cewa nan ba da daɗewa ba za a sanar da ranar bikin binne marigayi tsohon Ministan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Ogun - Tsohon ministan kuɗi a Najeriya, Dakta Onaolapo Soleye, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A wata sanarwa da iyalansa suka fitar ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023, tsohon ministan ya riga mu gidan gakiya da sanyin safiyar yau din nan da muke ciki.

Tsohon ministan kuɗi, Onaolapo Soleye, ya kwanta dama.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Ministan Buhari a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: ODG 23
Asali: Facebook

Dakta Soleye, wanda ya riƙe muƙamin Ministan kuɗi a lokacin mulkin soja na tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a 1980, ya mutu ne kwana huɗu bayan ya yi murnar cika shekara 90.

Kara karanta wannan

Innalillahi, Wani babban Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Bayanai sun nuna cewa Marigayin ya yi shagalin murnar ƙarin shekara ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya yi wa ƙasa hidima mai yawa

A rahoton Daily Trust, sanarwan ta ce:

"Da zuciya mai rauni tare da miƙa godiya ga Allah maɗaukakin Sarki, muna sanar da rasuwar Pa Dakta Onaolapo Soleye, mahaifin marigayi ɗanmu, Manjo Janar OO Soleye mai ritaya. Ranar Asabar ya cika shekara 90."
"Marigayi ya yi aikin hidima ga ƙasa da taimakon al'umma a muƙamai daban-daban da ya riƙe lokacin rayuwarsa kama daga kwamishinan ayyuka a Ogun, ministan kuɗi na tarayya da sauransu."
"Ya kasance mutum mai son Allah da ’yan Adam kuma yana da jajircewa a ayyukan Coci da kuma goyon baya da taimako ga duk wanda ya same shi, ta kowace hanya da zai iya."

Iyalan sun ƙara da cewa za a sanar da lokacin bikin ɓinne tsohon Ministan nan bada daɗewa ba, kafin nan sun roƙi al'umma su sanya marigayin a cikin addu'a.

Kara karanta wannan

Sabuwar guguwa ta tunkaro Ganduje da APC gabanin zaɓen 2027

Wani basarake a jihar Ogun ya rasu

A wani rahoton na daban Basaraken gargajiya a jihar Ogun, Oba Festus Oluwole Makinde, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 85 a duniya.

Rahotanni sun bayyana Sarkin ya rasu ne ranar Talata kuma fadarsa ta cika da masu zuwa jaje da ta'aziyya yau Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262