Karin bayani: Kamfanin Raba Wuta Ya Karyata Dauke Wuta a Kasar Saboda Yajin Aikin Yan Kwadago

Karin bayani: Kamfanin Raba Wuta Ya Karyata Dauke Wuta a Kasar Saboda Yajin Aikin Yan Kwadago

  • Ma'aikatan Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), da ke yajin aiki sun kashe babban layin lantarki na kasa
  • Sun yi hakan ne don yin mubaya'a ga yajin aikin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka shiga a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba
  • Ndidi Mbah, kakakin hukumar TCN, ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba
  • Sai dai kuma, a cikin wata sanarwa da TCN ya fitar, kamfanin ya bayyana rahotannin dauke wuta a kasar a matsayin kanzon kurege

Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), ta kashe babban layin lantarki na kasa a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, sakamakon ayyana yajin aikin sai baba ta gani da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dauki gagarumin mataki yayin da aka fara yajin aikin gama gari

Ndidi Mbah, kakakin TCN, ne ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai a safiyar ranar Talata, Daily Post ta rahoto.

Ma'aikataun wutan lantarki
Yajin aikin NLC: An dauke wutar lantarki a fadin Najeriya, har sai baba ta gani Hoto: TCN, Joe Ajaero, NLC
Asali: Facebook

A cewar Ndidi, ma'aikatan wutar lantarki, karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), sun bi umarnin kungiyar kwadago ta Najeriya na janye ayyukansu, kamar yadda PM News ta rahoto.

“Ma’aikatan wutar lantarki yan kungiyar kwadago ne; sun bi umarnin kungiyoyin kwadago na janye ayyukansu daga ranar Talata," inji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da sauran kungiyoyin da suka hada da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sun fara yajin aikin gama gari, bayan da suka bijirewa umarnin kotu na hana su shiga yajin aikin.

TCN ya karyata rahotannin dauke wuta a kasar

Sai dai kuma, a cikin wani sabon jawabi, shugabancin TCN ya bayyana rahotannin cewa an garkame kamfanin raba wuta saboda yajin aiki a matsayin "kanzon kurege".

Kara karanta wannan

NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta, Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

Sanarwar da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ya jaddada cewa babu gaskiya a cikin rahoton yayin da ya bayyana cewa layin raba wuta a kasar na nan yana aiki daram dam.

Kamfanin ya rubuta:

"Saboda haka kamfanin rarraba wuta na Najeriya na sanar da cewa wallafar Daily Post na zargin cewa Shugaban Hulda da Jama'a na TCN ya ce za a dauke wuta a kasa baki daya karya ce kuma yaudara ce gaba daya.
"Muna masu sanar da cewar layin lantarki na kasa na nan daram dam kuma yana rarraba wuta mai tarin yawa."

Legit Hausa ta tuntubi wasu yan Najeriya don jin ya lamarin wuta yake a bangarensu.

Malama Zainab daga yankin Chanchaga da ke jihar Neja ta tabbatar da yanzu haka suna da wuta. Ta ce:

“Bana tsammanin yan Nepa na yajin aiki don yanzu haka muna da wuta. Nima na zata sun shiga yajin aiki don da karfe 6:00 na asubahi suka dauke mana wuta amma zuwa karfe 12:00 na rana sai muka ga wutan ya dawo.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyoyin Kwadago sun shiga yajin aiki sai baba ta gani kan lakadawa shugaban NLC duka

Hakazalika, Malama Asiya da ke zaune a unguwar Brighter a garin Minna ta tabbatar da cewar ma’aikatan wuta na aiki.

"Wallahi har na shiga zullumi da na ji labarin yajin aiki, don tsorona Allah tsorona rashin wuta. Toh jiya-jiyan nan na yi kunun ayar siyarwa ai da an ja mun asara. Amma Alhamdulillah yanzu haka muna da wuta.”

FG ta dauki mataki kan yajin aiki

Gwamnatin tarayya ta dauki gagarumin mataki bayan kungiyar kwadago ta kaddamar da yajin aikin gama gari a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong, ya kira wani taro tare da shugabannin kungiyoyin TUC da NLC a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba.

Majiyar da ta bayyana wannan, ta bayyana a takaice:

"Ministan ya kira wani taron tattaunawa da kungiyoyin kwadago a ranar Talata."

NLC ta kira ma'aikatan wutan lantarki

A baya mun ji cewa kungiyar ‘yan kwadagon Najeriya ta umarci ma’aikatanta da su fara yajin-aikin sai baba-ta-gani a duk fadin kasar nan.

Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya ce yajin-aikin ya fara ne daga daren yau, tun daga 12:00 na tsakar daren Talatar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng