Peter Obi Ya Bai Wa Asibiti Gudunmawar Naira Miliyan 20, Ya Bayyana Dalili

Peter Obi Ya Bai Wa Asibiti Gudunmawar Naira Miliyan 20, Ya Bayyana Dalili

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayar da muhimmiyar gudunmawa ga wani asibiti a jihar Enugu
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya tabbatar da cewa ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 20 ga asibitin Mission Faith Foundation da ke Nsukka
  • Obi, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ya bayar da kuɗin ne don taimakawa wajen fara gina kwalejin jinya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Ɗan jam'iyyar Labour Party a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, ya ce ya bayar da gudummawar Naira miliyan 20 ga asibitin Faith Foundation Mission Hospital da ke jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Imo ta bayyana dalilin da ya sanya PDP, LP suka sha kaye a zaɓen gwamnan Imo

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne a cikin jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Peter Obi ya bayar da gudunmawa ga asibiti
Peter Obi ya bai wa asibitin Enugu gudunmawar N20m Hoto: @peterobi
Asali: Twitter

Meyasa Peter Obi ya ba da gudummawar Naira miliyan 20 ga asibitin Enugu?

Da yake magana kan dalilinsa na bayar da tallafin, Obi ya ce matakin ya yi daidai da kuɗurinsa na saka hannun jari a fannonin cigaban ƙasa da suka haɗa da lafiya, ilimi, da kawar da fatara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya bayar da tallafin ne domin kafa kwalejin ma'aikatan jinya.

A kalamansa:

"A ƙarshen mako na ziyarci garin Nsukka da ke Jihar Enugu, inda na bayar da gudummawar Naira miliyan 20 ga Asibitin Faith Foundation Mission dake Nsukka, hakan ya yi daidai da jajircewar da nake yi na saka hannun jari a fannonin da suka fi muhimmanci a cigaban ƙasa, wato kiwon lafiya, ilimi da kawar da talauci."

Kara karanta wannan

Zaɓabben Gwamna Usman Ododo ya magantu kan nasararsa a zaɓen Kogi, ya durƙusa a gaban Yahaya Bello

"Gudunmawar ita ce tallafi na farko ga asibitin ta hannun Bishop na Anglican na Nsukka, Rt Rev. Aloysius Agbo, don taimaka musu wajen fara gina kwalejin ma'aikatan jinya."
"Zan cigaba da tallafa wa ayyukan da za su kawo cigaba ga al'ummarmu, kuma za su kasance masu amfani ga ƴan Najeriya, don ta hanyar yin hakan, za mu iya gina sabuwar Najeriyar da muke fata. -PO"

Ƴan Obidients Sun Caccaki Peter Obi

A wani labarin kuma, magoya bayan Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP), sun fara caccakar ɗan takarar shugaban ƙasan bayan hukuncin kotun ƙoli.

Magoya bayan na Peter Obi sun fara caccakarsa ne saboda yadda ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel