Zabe Ya Kammala a Kogi, INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zabe, Ya Fi Kowa Adadin Kuri’u

Zabe Ya Kammala a Kogi, INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zabe, Ya Fi Kowa Adadin Kuri’u

  • Hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Kogi da aka yi a karshen makon nan
  • Usman Ododo ne ya lashe zaben da ya samu fafatawar 'yan takara daga jam'iyyun siyasa mabambanta
  • An kuma bayyana inda aka samu tsaiko, sai dai hakan bai shafi sakamakon zaben ba inji baturen INEC

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Kogi - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Usman Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, rahoton Tribune Online.

Baturen zabe Johnson Urama na Jami’ar Najeriya da ke Nssuka ne ya sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Lokoja, babban birnin jihar a daren Lahadi.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: a karshe, Dino Melaye ya yi martani kan dokuwa da yake a zabe, ya fadi abin da INEC za ta yi

An fitar da sakamakon zaben Kogi
Ododo ya lashe zaben Kogi | Hoto: Dino Melaye, Murtala Yakubu Ajaka (Muri Ajaka), Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: Facebook

Urama ya ce Ododo na APC ya samu kuri’u 446,237, yayin da babban abokin hamayyarsa, Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya samu kuri’u 259,052, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 46,362 yayin da Hon. Leke Abejide na jam'iyyar African Democratic Party (ADP) ya samu kuri'u 21,819.

Sanarwa daga bakin baturen zabe

A cewarsa:

"Bisa bin ka'idojojin doka, Ahmed Ododo bayan ya tabbatar wanda ya lashe zaben kuma shi ne zababben gwamna."

Ya kuma ce adadin kuri’un da aka soke a yankunan da ba a gudanar da zabe ba a jihar sun kai 16,247 kuma ba za su yi wani tasiri sosai ga sakamakon zaben ba.

Martanin Dino Melaye ga yadda bai samu kuri'u ba

A wani labarin, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi, Dino Melaye ya yi martani kan yadda zaben ke tafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Ajaka na SDP ya nemi a soke zaben gwamna a Kogi ta tsakiya

Melaye ya kiraye hukumar zabe ta INEC da ta soke wannan zabe na murdiya da ake yi, cewar TheCable.

Dino ya ce sakamakon zaben ya bayyana tun kafin a fara kada kuri'u a jiya Asabar 11 ga watan Nuwamba a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.