Kirsimeti: Gwamna Uno Ya Amince da Karin Albashin Wata Daya Ga Ma'aikatan Akwa Ibom
- Gwamna jihar Akwa Ibom ya amince da biyan ma'aikatan jiharsa albashin watan 13 domin su yi shagalin kirsimeti
- Fasto Umo Eno, ya ba da umarnin biyan kowane ma'aikaci kwatan-kwacin albashinsa a matsayin tallafin bikin kirsimetin 2023
- A watan Disamba na kowace shekara Kiristoci ke gudanar da bikin kirsimeti daga bisani kuma su yi murnar shigowar sabuwar shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon 0shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Akwa Ibom - Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya amince da ƙarin albashin wata ɗaya ga ma'aikatan jihar domin shagalin bikin Kirsimeti.
Gwamna Uno ya bada umarnin a biya ma'aikatan wannan ƙarin albashi a watan Disamba domin su samu damar gudanar da bukukuwan kirsimetin wannnan shekarar 2023.
Wannan garaɓasa na kunshe ne a wata sanarwa da Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Tuwita ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwan, Gwamnatin Akwa Ibom ta ce:
"Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Uno, ya amince da ƙarin albashin wata ɗaya wanda za a biya dukkan ma'aikatan jihar a watan Disamba domin shagalin bikin Kirsimeti."
Gwamnatin ta ƙara da cewa wannan albashin na watan 13 a shekarar 2023, za a bai wa ma'aikata ne a matsayin wata garaɓasa da kyauta da nufin taimaka musu.
Ta ce kuɗin zasu taimaka wa ma'aikatan su gudanar da shagulgulan bikin Kirsimeti wanda ake kira da, "yuletide" da kuma sabuwar shekara mai kama wa.
Da wannan ne Gwamna Uno na jam'iyyar PDP ya zama Gwamna na farko da ya fara sanar da tagomashin da zai ba ma'aikata a matsayin tallafin Kirsimetin bana.
Mabiya addinin Kirista na gudanar da bikin ne a karshen watan Disamba na kowace shekara, a ranar ɗaya ga watan Janairu kuma su yi bikin sabuwar shekara.
Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Kogi
A wani rahoton kuma Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya dira jihar Kogi domin goyon bayan Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP.
A wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa mai kunshe da Hotuna, an ga manyan jiga-jigan tare da juna.
Asali: Legit.ng