Zaben Gwamnan Kogi: Jami’an Tsaro Sun Kashe Yan Daban Siyasa 3, Sun Kwato Bindigogi

Zaben Gwamnan Kogi: Jami’an Tsaro Sun Kashe Yan Daban Siyasa 3, Sun Kwato Bindigogi

  • An samu hatsaniya a tsakanin jami'an tsaro da yan daban siyasa a Kogi yan kwanaki kafin zaben gwamna da za a gudanar a jihar
  • Jami'an tsaro sun murkushe yan daban siyasa uku sannan suka kama wasu bakwai a wani samame da suka kai mabuyarsu
  • A ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba ne al'ummar jihar Kogi za su fito su kada kuri'u domin zabar sabon gwamna bayan kammala mulkin Gwamna Yahaya Bello na shekaru takwas

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Kimanin kwanaki hudu kafin zaben gwamna a jihar Kogi, jami'an tsaron hadin gwiwa sun murkushe wasu da ake zaton yan daban siyasa ne su uku a Anyigba, yankin gabashin jihar.

Kara karanta wannan

Miyagu sun kai kazamin hari gidan babban jigon PDP kuma tsohon kwamishina, sun jefa bama-bamai

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda a jihar Kogi, SP William Ovye Aya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, rahoton Daily Post.

Jami'an tsaro sun murkushe yan bangar siyasa a jihar Kogi
Zaben Gwamnan Kogi: Jami’an Tsaro Sun Kashe Yan Bangar Siyasa 3, Sun Kwato Bindigogi Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jami'an tsaro sun kwato bindigogi a jihar Kogi

Kamar yadda Solace Base ta rahoto, Aya ya bayyana cewa jami'an tsaron sun kuma kwato bindigogin AK47 guda biyu daga hannun yan daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake bayyana cewa jami'an yan sanda, DSS da na NSCDC ne suka kai samamen a gidan da yan daban siyasar suke wanda jam'iyyun siyasa ne suka ajiye su, Aya ya kara da cewar mambobin tawagar biyu sun samu rauni sannan an kama mutum bakwai.

Wani bangare na sanarwar ta ce:

"Saboda haka, don yin zabe cikin lumana a jihar, za a ci gaba da kai samame mabuyar miyagun/yan daban domin hana su sukunin kai farmaki. Za a ci gaba da wannan aiki da ke gudana har zuwa bayan zaben, don Allah."

Kara karanta wannan

Babban Sarkin Yarbawa ya bayyana ma’anar tambarin da aka saba gani a hular Tinubu

Yan daba sun farmaki jama'a a Bayelsa

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan daban siyasa sun farmaki mambobin jam'iyyar PDP a karamar hukumare Nembe da ke jihar Bayelsa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, yan daban sun kashe wani mai suna Timi Biriyai Macdonald sannan sun jikkata wasu da dama ciki harda jigon jam'iyyar, Diepreye Akrisia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng