A Ƙarshe, Gwamnan APC Ya Bayyana Babban Abinda Ya Sa Shugaban NLC Ya Ci Duka a Imo
- A karshe, Gwamna Hope Uzodinma ya yi magana kan tsautsayin da ya faru har shugaban NLC na ƙasa ya sha wahala a jihar Imo
- Jim kaɗan bayan Bola Tinubu ya miƙa masa tutar APC a Villa, gwamnan ya zargi Joe Ajaero da tsoma hannu a siyasar jihar
- Ƙungiyar NLC ta zargi gwamnatin Imo da haɗa baki da ƴan sanda wajen sace shugabansu, lamarin da hukumar ƴan sanda ta musanta
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta zargi Uzodimma, da hada baki da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammed Barde, wajen “sace” shugabansu.
Abin da ya faru tun farko
A wata hira da ƴan jarida a farkon makon nan, shugaban NLC, Ajaero, ya zargi gwamnatin jihar Imo da “take hakkin ma’aikatan Najeriya a jihar."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon haka ya kudiri aniyar hada kawunan ma'aikatan jihar su fara yajin aikin sai baba ta gani, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da take maida martani, gwamnatin jihar Imo, ta ce zuwan Ajaero Owerri, babban birnin jihar, domin jagorantar zanga-zangar lumana ya saba wa umarnin kotu.
An ce wasu dakarun ‘yan sandan jihar Imo ne suka kama Ajaero a lokacin da yake jagorantar wata zanga-zanga a jihar ranar Laraba.
Sai dai rundunar ƴan sandan ta ce ba kama shi jami'ai suka yi ba, sun kubutar da shi ne kawai daga hannun wasu gungun mutane, suka ajiye shi a hannun su.
An ga Ajaero a cikin wani faifan bidiyo, yana zaune tsakanin wasu mutane biyu, yayin da aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Owerri.
Gwamna Uzodinma ya maida martani
Yayin da ya karbi tutar jam'iyyar APC daga hannun Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, Gwamna Uzodinma ya ce:
"Abin da ya faru a wannan yanayi mara daɗi shi ne shugaban kungiyar kwadago ta kasa dan asalin jihar Imo ne kuma ya gaza gane banbanci a tsakanin zama shugaban kungiya na ƙasa da tsoma hannu a siyasar cikin gida.”
Ƙila Tinubu ya rattaɓa hannu gobe Jumu'a - Abbas
A wani rahoton kuma kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, ya ce da yiwuwar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , ya rattaba hannu kan karin kasafin kudin 2023 ranar Juma’a.
Abbas ya bayyana haka ne ranar Alhamis bayan kudirin ƙarin kasafin kuɗin wanda ya kai N2.17tr ya tsallake karatu na uku a majalisar dattawa da majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng