An Kama Shugaban Matasa Kan Harin Da Aka Kai Gidan Kakakin Majalisar Jihar Ribas

An Kama Shugaban Matasa Kan Harin Da Aka Kai Gidan Kakakin Majalisar Jihar Ribas

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke shugaban majalisar matasa ta kasa (NYC) reshen jihar Ribas
  • Ambasada Chijioke Ihunwa ya jagoranci matasa sama da 120 zuwa gidan kakakin majalisar jihar Ribas don tada kayar baya
  • Rundunar 'yan sanda, ta tsaurara matakan tsaro a ginin majalisar dokokin jihar Ribas da gidan kakakin majalisar jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ribas - Rundunar 'yan sandan Jihar Ribas, a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, ta ce ta cafke tare da tsare shugaban majalisar matasa ta kasa (NYC) na jihar Ribas, Chijioke Ihunwo, biyo bayan wani hari da aka kai gidan kakakin majalisar dokokin jihar Martins Amaewhule.

Gwaman jihar Ribas Siminalayi Fubara
Shugaban matasa a Ribas ya shiga hannun hukuma kan zargin kai hari gidan Kakakin Majalisa. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, sashen rundunar da ke binciken manyan laifuka na jihar (SCID) ya tsare shugaban majalisar tare da wasu matasa 122, kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda Grace Iringe-Koko ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, yayin tabbatar da kama matasan.

Kara karanta wannan

Sokoto: Yan sanda sun magantu kan rahotannin kama yan bindiga da ya bazu a dandalin sada zumunta

Abunda rundunar 'yan sanda tace game da kai hari gidan Martins Amaewhule

Rundunar 'yan sandan ta ce Ihunwo ya jagoranci matasa "da nufin tada kayar baya" tare da kuma yi wa gidan kakakin majalisar jihar tsinke "da ke a rukunin gidajen Forces Avenue, tsohuwar GRA, Fatakwal, inda suka kutsa kai cikin gidan ta karfin tsiya, wanda ya yi sanadiyar lalata kofar shiga gidan".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sandan ta kara da cewa:

A yayin da suke kan aikata wannan danyen aikin, mun samu kiran gaggawa kan lamarin, inda nan take muka tura jami'anmu gidan kakakin majalisar. Bayan isar su, sun samu nasarar cafke matasa 122, ciki harda shi Amb. Chijioke Ihunwo.
Bayan cafke wadanda ake zargin, an kai su sashen rundunar da ke kula da manyan laifuka ta jihar (SCID) da ke garin Fatakwal, domin ci gaba da gudanar da binciken sirri.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke yarinya mai shekaru 14 kan zargin yi wa lakcara yankan rago a jihar Neja

Haka zalika, rundunar yan sandan ta ce ta tsaurara matakan tsaro a farfajiya da wajen ginin majalisar dokoki ta jihar, da kuma gidan kakakin majalisar, da wasu muhimman wurare a jihar, domin dakile faruwar wata tarzoma a nan gaba.

Ƴan Majalisa Sun Zaɓi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin a Jihar Ribas

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto muku yadda wani tsagi na majalisar dokokin jihar Ribas suka yi sabon zabe, inda suka zabi Ehie Edison, a matsayin sabon kakakin majalisar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.