Dan Najeriya Ya Siya Wayar iPhone 15 Amma Ya Tarar da Teba a Kwalin, Ya Koka a Bidiyo

Dan Najeriya Ya Siya Wayar iPhone 15 Amma Ya Tarar da Teba a Kwalin, Ya Koka a Bidiyo

  • Wani mutumi da ya siya iPhone ya koma gida sai ya ga ashe teba aka siyar masa a cikin kwali
  • Mutumin ya koka a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya yayin da yake dudduba teban da aka siyar masa a maimakon waya
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun tambayi yadda mutum zai iya yin wannan kuskure na kin duba abun da aka siyar masa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullunm.

Wani bidiyo ya yadu a soshiyal midiya wanda ke nuna wani mutum cike da nadamar zuwa siyan wayar iPhone 15 a kasuwar 'Computer Village.

Bayan ya siya wayar iPhone, ya bude kwalin kawai sai ya ga teba nade a cikin kwalin don sa shi ya yi nauyi kamar da gaske akwai abu a ciki.

Kara karanta wannan

Bidiyon jami’ar yar sanda tana rera taken kasa cike da kura-kuraiya girgiza intanet

Teba a cikin kwalin wayar iPhone
Wani Mutum da Ya Siya iPhone 15 Ya Gano Teba a Ciki, Ya Koka a Bidiyo Hoto: @therealdotun
Asali: TikTok

Diramar iPhone 15 a Najeriya

A cikin bidiyon, an jiyo wata murya tana korafin cewa yanayin kwalin ya banbanta. Duk da kasancewar abinci a ciki, kwalin na nade a cikin wata farar leda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun yi mamakin dalilin da yasa mai siyar wayar bai yi tunanin duba kwalin ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon iPhone mai teba

@OmoAdigun_ ya ce:

"Mutumin ya je ya nemi miyar taushe mai kyau don Allah."

@MensahEstherOmo ya ce:

"Nemi miya computer Village ya nuna maka sannu dan uwa."

flameoceanstech ya ce:

"Nawa ya biya. Ba ku ma iya karya ba.. shin wannan ne kwalin iPhone 15 pro max?"

ubigho_omena ta nuna shakku kan lamarin:

"Wannan shiri ne don Allah wato baka bude don ganin abun da ka siya ba a gaban mai shi? Ci gaba da wasa."

Kara karanta wannan

An yi ruwan daloli, bidiyo ya nuna yadda attajiri ya hau jirgi ya sako kudi, an yi warwaso

big__rosey ta ce:

"Ka siya waya baka bude shi a wajen? Odigweugu."

mayorsoj ya ce:

"Miyan taushe zai tafi sosai da wannan magana ta gaskiya."

Yar sanda ta rera taken kasa cike da kura-kurai

A wani labarin, mun ji cewa masu kallo da dama sun girgiza yayin da wata jami'ar yar sanda ta rera wakar taken kasar cike da kura-kurai a wani taron manyan jami'an yan sanda a Owerri, jihar Imo.

Bidiyon jami'ar yar sandar tana tsallake wasu baitoci wajen rera taken kasar ya yadu a dandalin soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng