Tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Ben Nwabueze, Ya Rasu Yana da Shekaru 92
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Farfesa Ben Nwabueze (SAN), fitaccen lauya na kundin tsarin mulkin Najeriya kuma tsohon babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ya rasu.
Arinze Nzeli, shugaban kungiyar Atani Town Union ne ya sanar da rasuwar, yana mai cewa fitaccen lauyan ya rasu a gidansa da ke Legas misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, rahoton The Nation.
Nzeli ya ce kwararren lauyan ya dauki dan lokaci yana fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.
Dan majalisa ya tabbatar da rasuwar Nwabueze
Afam Ogene, dan majalisar tarayya mai wakiltar Ogbaru, shima ya tabbatar da rasuwar cikin sakon kar ta kwana, yana mai cewa tsohon Sakataren na Ndigbo Worldwide ya rasu a ranar Lahadi.
Ya rasu yana da shekaru 92.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ben Nwabueze dan asalin garin Atani ne daga jihar Anambra. Babban lauya ne a Najeriya mai mukamin SAN, sannan an haife shi ne a 1931.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng