Ibtila'i: Jirgi Dauke da Mutane Fiye Da 100 Ya Kife a Tsakiyar Rafi Taraba, Bayanai Sun Fito

Ibtila'i: Jirgi Dauke da Mutane Fiye Da 100 Ya Kife a Tsakiyar Rafi Taraba, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa wani adadin mutane da ba a tabbatar ba sun bace bayan wani jirgin ruwa da ke dauke da fasinjoji fiye da 100 a Rafin Benue da ke karamar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba ya kife a tsakiyar ruwa
  • An gano cewa mafi yawancin mutanen da ke cikin jirgin ruwan suna dawowa ne daga kasuwar kifi ta Mayoreneyo
  • Hatsarin ya faru ne a ranar Asabar, 28 ga watan Oktoba, a hanyar zuwa garin Binnari da ke karamar hukumar Karim Lamido

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Taraba - Jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 100 ya kife a tsakiyar ruwa a Rafin Benue a ranar Asabar.

Yan kasuwa, mata da yara da ke hanyar zuwa garin Binnari da ke karamar hukumar Karim-Lamido na jihar na cikin jirgin ruwan da abin ya faru da shi.

Kara karanta wannan

Ya kamata CBN ta sa a daina amfani sabbin takardun Naira da Buhari ya kawo, malami ya fadi dalilai

Jirgin ruwa ya kife da fasinjoji fiye da 100 a Taraba
Ana fargabar fasinjoji 100 sun nutse bayan jirgin ruwa ya kife da su a Taraba. Hoto: Ifeomaohiriblog
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu da dama cikin fasinjojin sun baro Mayoreneyo misalin karfe 3.30 na yamma sannan ya kife kimanin mintuna 40, a cewar majiyoyi.

Wani mazaunin Mayoreneyo, Musa Mayoreneyo, ya fada wa Daily Trust cewa jirgin ruwan da abin ya ritsa da shi ya kwaso fasinjoji da Binnari zuwa Mayoreneyo kafin faruwar lamarin.

Hatsarin Rafin Benue: 'Gawar mutane biyu kawai aka gano'

A hirar wayar tarho, wani mazaunin Binnari, ya ce:

"A halin yanzu da na ke magana da kai, gawar mutum biyu cikin fasinjojin kawai masu ninkaya a yankin suka gano."

Wata majiya daga Mayoreneyo ya fada wa wakilin majiyar Legit Hausa cewa babu wani fasinja da ke sanye da 'rigar ruwa' a lokacin da abin ya faru.

Ciyaman din riko na kungiyar masu jigilar mutane a jirgin ruwa na jihar Taraba, Jidda Mayoreneyo, ya fada wa Daily Trust cewa an gano gangan jikin mutane 15 kusa da wurin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Basarke Da Mutum 5 a Zamfara

Da ya ke tabbatar da lamarin, Ciyaman, na kwamitin riko na Ardo-Kola, Alhaji Dalhatu Kawu, ya bayyana abin a matsayin abin bakin ciki.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, SP Abdullahi Usman, ya ce bai riga ya samu rahoton faruwar lamarin ba.

Mutum Biyu Sun Riga Mu Gidan Gaskiya, Wasu 4 Sun Jikkata Yayin Da Jirgin Ruwa Ya Kife a Legas

A wani rahoton, wasu mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sannan wasu hudu sun samu rauni sakamakon jirgin ruwa da ya nutse da su a garin Isawo, karamar hukumar Ikorodu a jihar Legas.

Ololade Agboola, mataimakin mai magana da yawun hukumar kashe gobara da ayyukan ceto na jihar Legas ya tabbatar da afkuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164