"Ta Sha da Kyar": An Ceto Wata Akuya Bayan Ta Saka Kanta a Butan Karfe, Bidiyon Ya Yadu

"Ta Sha da Kyar": An Ceto Wata Akuya Bayan Ta Saka Kanta a Butan Karfe, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata akuya ta kusa haduwa da ajalinta bayan ta makale a jikin wani butan karfe, wanda yasa ta dungi numfasawa da kyar
  • A wani bidiyo da ya yadu, an gano yadda mutane suka taru domin taimakawa akuyar wajen fitar da ita daga butan
  • Bayan an yi nasarar fitar da ita, akuyar ta ruga a guje sannan ta bace daga wajen cikin yanayi mai ban dariya

An yi nasarar ceto wata akuya da kanta ya makale a cikin wani buta bayan makwabta sun taru a wajen.

A cikin wani bidiyo mai ban dariya da ya yadu a soshiyal midiya, alamu sun nuna akuyar tana neman abun sakawa a baki a cikin butan.

Kan akuya makale a cikin buta
An Ceto Wata Akuya Bayan Ta Saka Kanta a Butan Karfe, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Twitter/@AkpraiseMedia
Asali: Twitter

Ta taki rashin sa'a yayin da kanta ya makale a cikin butan, sannan ta dungi fama wajen numfasawa.

Kara karanta wannan

“A Dunga Hankali da Yan Aiki”: Wasu Iyali Sun Kadu Bayan Kama Mai Aikinsu a Wajen da Bai Kamata Ba a Gida

An ceto akuya bayan kansa ya makale

Akuyar tana ta gudu kanta makale a cikin butan, tana kokarin samun mafita amma fafur abun ya ci tura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Allah ya tarbawa garin akuyar nono lokacin da wasu makwabta suka taru a wajen sannan suka fara neman mafita kan lamarin.

A karshe, an fitar da kan akuyar ta karfi da yaji, sannan ta yi gaggawan barin wajen a guje. Shafin @AkpraiseMedia ne ya wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da akuya ta makale

@official_adags ya ce:

"Nan gaba, idan akuyar nan ta ga buta ko ma tukunya ba ba zai sake kusantarsa ba a rayuwarsa.:

@official_adags ya yi martani:

"Daga karshe akuyar nan ya ga abun da ta dade yana nema."

@EmaazDr:

"Ta yaya kan ya isa wajen nan?"

Kara karanta wannan

An Tsinci Gawar Wata Dalibar Najeriya Da Ta Mutu a Dakin Saurayi

@CalebOkike1:

"Akuyar nan za ta yi bayani har ta gaji."

@Gen2stephen ta ce:

"Dabba ba zai taba sauyawa daga dabba ba."

An kama yar aiki tana haura taga

A wani labari na daban, wasu iyali sun kama mai yi masu aikin share-share tana kokarin shiga cikin gidansu ta taga.

Iyalin sun ce sun lura cewa yarinyar tana haurawa cikin gidan ta taga a duk lokacin da masu gidan basa nan.

An tattaro cewa an dauko hayar yarinyar ne domin ta dunga share harabar gidan kawai, amma sai aka kama ta tana shiga cikin ainahin gidan ta taga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng