Najeriya da Kasashe 119 Sun Amince da Kudurin Falasdinawa, Sun Yi Kira da a Tsagaita Wuta
- Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri'u kan yadda za a kawo karshen tashin-tashina a tsakanin Hamas da sojin Isra'ila
- Yakin Hamas da Isra'ila ya kai ga mutuwar Falasdinawa da yawa, hakan na ci gaba da daukar hankalin duniya
- Najeriya na daga kasashen da suka bayyana goyon bayansu kan tsakaita wuta da Isra'ila ke yi kan mutanen Gaza
Najeriya da wasu kasashe 119 ne a ranar Juma'a suka kada kuri'ar amincewa da kudurin da ke kira da a samar da "zaman lafiya mai dorewa" tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas a Gaza.
Har ila yau, tanasun amince da ci gaba da shigar da kayayyakin agaji da rayuwar yau da kullum a yankin na Zirin Gaza mai fama da takurar Isra'ila, rahoton Al-Jazeera.
Kudirin da kasashen Larabawa suka shirya ya samu kuri'u 120 na goyon baya, 14 na adawa da kuma 45 suka ki bayyana matsayarsu.

Kara karanta wannan
Gaza: Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Zargi Isra'ila Da Keta Dokokin Jin Kai

Asali: UGC
Makasudin kudurin da aka amince dashi
Kudirin da a yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta amince dashi matsaya ta mafi yawan ra'ayi na kasashe mambobin majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
To sai dai kuma wannan shi ne martanin farko a hukumance da Majalisar Dinkin Duniya ta yi tun bayan da Hamas ta kai hari kan Isra'ila da kuma martanin taron dangin da Isra'ila din ta ke ci gaba da yi.
A baya, wasu kasashe sun mika kudurin Majalisar Dinkin Duniya ta fito tare da yin Allah-wadai da harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.
Yadda aka kashe Falasdinawa
A halin da ake ciki, Isra'ila ta kashe adadi mai yawa na Falasdinawa da ke rayuwa a Zirin Gaza tun bayan fara daukar martani ga harin Hamas.
An bayyana yadda a baya sojin Isra'ila suka farmaki asibitin da ya kai ga mutuwar kananan yara da mata masu yawa.

Kara karanta wannan
Bashin $3.5bn: Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kasafta Kudaden Don Amfanar Talakawa, Ya Fadi Tsawon Lokacin Biya
Ba yanzu gaba da fadace-fadace suka fara ba a yankin, hakan ya faro ne tun shigar Isra'ila yankin Gabashi tun bayan yakin duniya na biyu.
Biden ya ba da agaji ga Gaza
A wani labarin, shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya ba da gudumawar Dala miliyan 100 don taimakawa Gaza.
Biden ya ba da taimakon ne bayan ya dira a yankin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra’ila da Kungiyar Hamas, cewar TheCable.
Shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba 18 ga watan Oktoba bayan rikicin da ya barke.
Asali: Legit.ng