Mutum Biyu Sun Mutu, Huɗu Sun Jikkata Yayin da Jirgin Ruwa Ya Kife a Legas
- An rasa rayuka yayin da wani jirgin ruwa ya kife a yankin ƙauyen Isawo da ke ƙaramar hukumar Ikorodu a jihar Legas
- Mutum biyu mata ake tsammanin sun mutu sanadin kifewar jirgin ruwa yayin da wasu huɗu kuma suka jikkata
- Daraktan hukumar kashe gobara da aikin ceto ta jihar ta jaddada buƙatar kauce wa duk abin da ya saɓa doka a ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Lagos - Rahotanni sun bayyana cewa mutum biyu sun mutu, wasu huɗu sun jikkata yayin da wani Jirgin ruwa ya nutse da mutane a ƙauyen Isawo, ƙaramar hukumar Ikorodu ta jihar Legas.
Mataimakin mai magana da yawun hukumar kashe gobara da ayyukan ceto na jihar Legas, Ololade Agboola, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.
Ya bayyana cewa jami'an hukumar sun samu nasarar ceto matan da suka kai munzali huɗu cikin ƙoshin lafiya bayan haɗarin ya rutsa da su, Daily Trust ta ruwaito.
Yadda haɗarin ya faru
Ya ce hukumar ta samu labarin faruwar haɗarin da misalin ƙarfe 8:16 na dare kuma nan take ta tura tawagar jami'an ceto domin zakulo mutanen da suka nutse.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, jami'an sun haɗa kai da waɗan da suka san ruwa na gargajiya a aikin ceton, kuma duk da dare ya yi, haka aka ci gaba da aikin lalube har zuwa ƙarshen daren sannan aka tashi.
A rahoton Dailypost, Agboola ya ce:
"Tawagar jami'an sun sake komawa suka ci gaba da aikin zaƙulo waɗanda suka ɓata. Bisa rashin sa'a aka tsamo gawar mata biyu, Misturat Okunbanjo, yar shekara 18, da Azeezat Amoo, mai shekaru 16."
"Daga ƙarshe an karkare aikin ceton da misalin ƙarfe 10:10 na safiyar ranar Jumu'a."
An ja hankalin mutane
Darektan hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta bayyana nadamarta dangane da wadanda ake zargin sun mutu.
Ta jaddada mahimmancin gujewa ayyukan da suka saɓa doka a ruwa tare da bayyana kokarin da ake yi na ilimantarwa da wayar da kan al’umma kan matakan hana faruwar hakan.
Mutane Sama da 20 Sun Jikkata a Kaduna
A wani labarin kuma Wata tanka da ke kokarin sauke kayan man fetur a gidan mai a Hayin Rigasa ta fashe ta kama wuta ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna akalla mutane 20 suka ji raunuka cikinsu har da jami'an kwana-kwana, yan bijilanti da masu wuce wa.
Asali: Legit.ng