Mutane Sama da 20 Sun Jikkata Yayin da Wani Abu Ya Fashe a Jihar Kaduna

Mutane Sama da 20 Sun Jikkata Yayin da Wani Abu Ya Fashe a Jihar Kaduna

  • Wata tanka da ke kokarin sauke kayan man fetur a gidan mai a Hayin Rigasa ta fashe ta kama wuta ranar Laraba
  • Rahotanni sun nuna akalla mutane 20 suka ji raunuka cikinsu har da jami'an kwana-kwana, yan bijilanti da masu wuce wa
  • Daraktan hukumar kashe gobara reshen jihar Kaduna ya ce yanzu haka waɗanda suka ji raunuka suna karban magani a asibiti

Jihar Kaduna - Aƙalla mutane 20 ne suka ji raunuka bayan wata Tanka ɗauke da man Fetur ta fashe ta kama da wuta a wani gidan mai a hayin Rigasa, ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.

Rahoton jaridar Punch ya tattaro cewa mutanen da suka ji raunuka daban-daban sakamakon fashewar sun haɗa da jami'an hukumar kashe gobara 5, ƴan bijilanti da masu wucewa.

Fashewar tanka ya yi sanadin jikkata wasu mutane 20.
Mutane Sama da 20 Sun Jikkata Yayin da Wani Abu Ya Fashe a Jihar Kaduna Hoto: punchng
Asali: UGC

Jami'an hukumar kashe gobara da ibtila'in ya rutsa da su yayin ƙoƙarin kashe wutar, yanzu haka suna asibitin Barau Dikko da ke cikin birnin Kaduna.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

Halin da mutane suka shiga

Daraktan hukumar kwana-kwana na jihar Kaduna, Mista Paul Aboi, shi ne ya tabbatar da haka ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa Tankar na tsaka da sauke man fetur ɗin da ta ɗauko a gidan mai a lokacin da ibtila'in ya faru, bisa haka wuta ta kama ranar Laraba.

Ya dora alhakin faruwar lamarin a kan sakaci daga bangaren gidan man, inda ya ce bai kamata a yi aikin sauke man da tsakar rana ba.

Ya kuma gargadi masu gidan man fetur da su guji jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar sauke mai a daidai lokacin da ya dace watau idan rana ta yi sanyi, da yamma.

Wata mata ta koka da cewa wutar da ta kama sakamakon fashewar tankar, ta taɓa gidan danginta da ke kusa da gidan man.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wasu Hatsabiban 'Yan Fashi Biyu Suka Tsere Daga Gidan Yari a Jihar Arewa

Ta kara da cewa dan uwanta da dansa na cikin mawuyacin hali saboda tsananin kunar da suka yi sanadin fashewar tankar.

Har zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton, hukumar ƴan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara

A wani rahoton na daban 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garin Maru, hedkwatar ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun shiga fadar mai martaba Sarkin Maru amma Allah ya sa ya tsallake sharrinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262