DHQ: Luguden Wutan Jirgin Yakin Sojojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga Sama da 100
- Sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 100 a wani ruwan bama-bamai da suka yi a iyakar jihohin arewa biyu
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya, sojoji sun aika gomman da yan bindiga lahira, sun damƙe wasu
- Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya jero wasu nasarorin da sojoji suka samu cikin mako ɗaya
FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun soji sun sheƙe 'yan ta'adda sama da 100 a wani luguden wuta ta sama a iyakar jihohin Zamfara da Neja.
Jami'in hulɗa da jama'a na hedkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ne ya faɗi haka ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi kan ayyukan da rundunar soji ta yi a faɗin sassan ƙasar cikin makon da ya gabata, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake nuna hotunan nasarorin da rundunar sojojin saman Najeriya suka samu, ya ce ruwan bama-baman ya kuma ragargaji mahara da dama a wasu sassan kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙarin nasarorin sojoji a mako ɗaya
Buba ya ƙara da cewa a wani samame da dakarun soji suka kai gidan kwamandan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Neja, sun kama mayaƙa da dama tare da kwato kayyaki.
Ya ce a wasu ayyukan da sojoji suka gudanar a makon da ya gabata a sassa daban-daban na ƙasar nan, sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 73 tare da kama wasu 182.
A cewarsa, sojojin sun kuma kama wasu mutane 14 da ake zargin barayin mai ne, tare da kubutar da mutane 68 da aka yi garkuwa da su a yankin Kudu-maso-Kudu.
Kakakin DHQ yace dakarun sun daƙile yunkurin satar man da aka kiyasta ya kai na kimanin Naira biliyan 1.212 a kasuwancin haram.
“Bugu da kari, sojojin sun kwato makamai iri-iri 119 da alburusai kala daban-daban 1,537," in ji shi.
Mutane 18 Sun Tsallake Rijiya da Baya
A wani rahoton na daban Fasinjoji akalla 18 sun tsallake rijiya da baya yayin da mummunan hatsarin mota ya rutsa da su a babban titin Legas zuwa Ibadan.
Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan motar Bas mai cin mutum 18 ta taso daga Maryland a Legas ta nufi birnin Ibadan.
Asali: Legit.ng