Hukumar DSS Ta Saki Tsohon Shugaban EFCC Bawa, Bidiyo Ya Bayyana
- Daga karshe tsohon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaki iskar yanci daga hannun DSS
- Rundunar tsaron farin kaya ta sako tsohon shugaban na EFCC a daren ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, bayan kwanaki 134 a tsare
- Wani bidiyo da ke tabbatar da sakin Bawa ya bayyana a soshiyal midiya yayin da aka gano shi tare da yan uwansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Rahotanni sun kawo cewa rundunar tsaron farin kaya (DSS) ta saki tsohon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, bayan ya shafe kwanaki 134 a tsare.
Jaridar Punch ta tabbatar da ci gaban a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya a daren ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba.
Rundunar tsaron farin kayan ta kama Bawa a ranar 14 ga watan Yuni, awanni bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi.
Bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya yayin aka saki Bawa, ya hadu da yan uwansa
Kalli bidiyon a kasa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan Najeriya sun yi martani kan sakin Bawa
@Peter81927970 ya yi martani:
"Ya yi masa kyau. Amma menene laifinsa?"
@KennyNuga ya ce:
"Labari mai dadi...An saki Abdulrasheed Bawa."
@Sadimr_real ya yi martani:
"Allah ya saka masa kawaii."
@MukhtarBaura ya ce:
"Alhamdullah ."
@IshaqHosney ya ce:
"Masha Allah."
@fashemmy2010
"Lallai tattaunawar sirri da dama ne suka yi sanadiyar samun yancinsa."
@iAbdullaaah
"Na taya shi murna ."
@SadiqIA1
"Yanzu ya zama tsohon shugaba."
@Ibrahee66616215
"Kasar da bata da doka allah yasakama bawa."
@Algeriaand25901 ya ce:
"Shi at dadin inkasamu kayiwa 'yan uwa."
@oriadeDplug
"Zai yi takarar kujerar shugabanci a gaba."
@Kabir_Y_
"DSS ta tsare mutum na kimanin kwanaki 134 ba tare da laifi ko daya ba."
Bawa ya yi murabus daga shugabancin EFCC
A baya mun ji cewa Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ya yi murabus daga matsayinsa.
Fadar shugaban kasa ce ta sanar da murabus din Bawa a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.
A cikin sanarwar, Ngelale ya sanar da nadin Ola Olukoyede da Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin sabon shugaba da sakataren hukumar.
Asali: Legit.ng