Mutane 18 Sun Tsallake Rijiya da Baya a Babban Titin Ibadan-Legas
- Fasinjoji akalla 18 sun tsallake rijiya da baya yayin da mummunan hatsarin mota ya rutsa da su a babban titin Legas zuwa Ibadan
- Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan motar Bas mai cin mutum 18 ta taso daga Maryland a Legas ta nufi birnin Ibadan
- Wasu fasinjojin motar sun ce Allah ne kaɗai wanda ya taimake su har suka tsira da rayuwarsu ta hanyar ƙoƙarin direba
Lagos - Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 18 ne suka tsallake rijiya da baya-baya a wani hatsarin Mota da ya rutsa da su a sashin doguwar gadar da ke kan titin Legas zuwa Ibadan.
A rahoton jaridar The Nation, motar Bas Mazda mai ɗaukar mutum 18 ta taso daga tashar Maryland zuwa Ibadan, jihar Oyo ɗauke da fasinjoji lokacin da hatsarin ya auku.
Wannan mummunan hatsari ya afku ne yau Laraba 25 ga watan Oktoba, 2023 a kan babban titin Legas zuwa Ibadan, amma Allah ya tseratar da fasinjojin da ransu.
Ɗaya daga cikin Fasinjojin motar, mahaifiyar jariri ɗan watanni shida a duniya ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba don taimakon Allah ba, da kokarin direban motar da yanzu na zama gawa. Muna ƙara gode wa Allah da direba bisa ceton rayuwarmu."
Wani fasinja mai suna Abubakar da ke hanyar zuwa jihar Kebbi amma ya shirya sauka a Ibadan, ya yi ikirarin cewa kudin da yake da shi ba zai iya kai shi garin da ya nufa ba.
Mutumin ya kuma koka kan cewa ya fi kowane fasinjar cikin motar shiga yanayin takaici, amma Allah ya taimaka sun tsira da rayuwarsu.
A ruwayar Punch, Mutumin ya ce:
“Na fi kowa bakin ciki a wannan motar bas, kudin da ke tare da ni ba za su iya kai ni Kebbi ba. Direban ya karbi Naira 2,600 kafin mu baro tasha, kuma ba shi da niyyar dawo mana da kudin."
"Babu alamar za a dawo mana da kuɗin mu ko kuma direban ya kira a kawo masa agajin motar da zata kwashe fasinjojin."
Yayin haɗa wannan rahoton an ga jami'an tsaro kamar yan sanda da jami'an hukumar kiyaye haɗurra na aikin bada hannu don kar masu tahowa su biyo wajen.
Ƴan fashi sun tsere daga Kurkuku
A wani rahoton kuma Mazauna cikin garin Katsina sun shiga tashin hankali bayan wasu hatsabiban 'yan fashi sun tsere daga gidan gyaran hali.
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida, inda ta ce har ta sake kama ɗaya daga ciki.
Asali: Legit.ng