Kotu Ta Tsige Sarkin Masarautar Ogbomoso a Jihar Oyo, Ta Umarci a Nada Sabo

Kotu Ta Tsige Sarkin Masarautar Ogbomoso a Jihar Oyo, Ta Umarci a Nada Sabo

  • Babbar Kotun jihar Oyo ta sauke Oba Ghandi Olaoye daga matsayin Sarkin Ogbomoso wanda ake kira da Soun
  • Alkalin Kotun ya bayyana cewa tsarin da aka bi wajen naɗa sabon Soun na Ogbomoso ya saɓa ƙa'idaz ya umarci a canza zaɓe
  • A watan Satumba, 2023, gwamnatin Oyo ta sanar da naɗa Fasto a kujerar Sarautar mai daraja

Jihar Oyo - Babbar Kotun jihar Oyo mai zama a Ogbomoso, a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, 2023, ta rushe naɗin Sarki watau Soun na Ogbomoso, Oba Ghandi Olaoye.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa gwamnatin jihar Oyo ta sanar da naɗin Faston cocin Redeemed, Olaoye, a matsayin sabon Sarkin babbar masarautar Ogbomoso, wanda ake kira 'Soun'.

Kotu ta sauke Soun na Ogbomoso daga kan karagar mulki.
Kotu Ta Tsige Sarkin Masarautar Ogbomoso a Jihar Oyo, Ta Umarci a Nada Sabo Hoto: punchng
Asali: UGC

Bayan haka ne kuma aka yi bikin naɗa sabon Sarkin a kan karagar mulki ranar 8 ga watan Satumba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Aminu Tambuwal a Matsayin Sanata PDP

Amma da take yanke hukunci yau Laraba, babbar Kotun ta tsige sabon Sarkin daga kan karagar mulki, ta kuma bada umarnin a bi matakan da ya dace wajen naɗa sabo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda shari'ar ta samo asali

Kafin yanzu, daya daga cikin ‘yan takarar da suke nemi zama Sarki, Yarima Kabir Laoye ya garzaya kotu yana kalubalantar tsarin zaben da ya kawo Ghandi a matsayin sabon Soun.

A baya dai kotun ta bayar da umarnin kada gwamnatin jihar Oyo ta sanar da kowa a matsayin sabon Soun har sai an gama shari’ar da ke gaban kotu.

Amma duk da haka gwamnatin jihar ta yi watsi da umarnin kotu inda ta sanar da Ghandi Laoye a matsayin sabon Soun na Ogbomoso kuma ana naɗa masa rawani.

Yarima Kabir Laoye ya ce tsarin da aka bi aka naɗa Gandhi ya saɓa ka'ida, ina ya roƙi Kotu ta soke naɗin sabon Soun kana ta yi umarnin a sake sabon tsarin zabe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Kori Daraktocin Hukumar NIWA, NSC Ya Maye Gurbinsu

Mai shari’a Adedokun yayin da yake yanke hukuncin ya ce tsarin zaben da kuma naɗa Laoye ya sabawa doka. Ya umarci sarakunan Ogbomosho da su koma su zaɓo sabon sarki.

Tambuwal ya yi nasara a Kotu

A wani rahoton na daban Kotun zaɓe ta tabbatar da nasarar Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP a zaɓen Sanatan Sokoto ta kudu.

Ɗan takarar APC, Abdullahi Ɗanbaba ne ya kalubalanci sakamakon zaben da INEC ta bayyana bisa zargin saɓa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262