An Daɓa Wa Wata Daliba Wuka Har Lahira a Dakin Kwana a Jihar Gombe

An Daɓa Wa Wata Daliba Wuka Har Lahira a Dakin Kwana a Jihar Gombe

  • Wasu mutane da ba a gano ko su waye ba sun kashe ɗalibar kwalejin horas da malamai NCE ta jihar Gombe
  • Rahotanni sun bayyana cewa makasan sun bi ɗalibar har ɗakinta na kwana da ke garin Billiri, suka soka mata wuƙa har lahira
  • Hukumar 'yan sanda reshen jihar Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa tuni jami'anta suka fara bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Gombe - Wasu makasa da ba a sani ko su waye ba sun caccaka wa ɗalibar aji na uku (NCE III) a kwalejin ilimi ta jihar Gombe wuƙa har lahira a ƙaramar hukumar Billiri.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, makasan sun bi sawun ɗalibar har zuwa ɗakin kwananta na wajen makaranta da ke Unguwar Zazzagawa a garin Billiri a karshen makon nan.

An kashe wata daliba a jihar Gombe.
An Daɓa Wa Wata Daliba Wuka Har Lahira a Dakin Kwana a Jihar Gombe Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Mazaunin Unguwar ya bayyana cewa makasan da har yanzu ba a tantance su waye ba sun kashe ɗalibar da safiyar ranar Lahadi kuma suka gudu bayan aikata kisan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Ga Ta Kansu Yayin da Jami'an Tsaro Suka Kutsa Cikin Daji, An Samu Babbar Nasara a Arewa

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Gombe (PPRO), ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa makasan sun yi amfani da wuƙar ɗakin girki, suka burma wa ɗalibar har Allah ya mata rasuwa.

Yan sanda sun fara bincike

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa tuni jami'ai suka kaddamar da bincike domin gano waɗan da suka aikata wannan ɗanyen aiki, su girbi abin da suka shuka.

Ya ce jami'ai sun ɗauki gawar ɗalibar sun kai ta ɗakin ajiyar gawarwaki sun ajiye gabanin kammala binciken da suka fara kan lamarin.

A 'yan watannin nan ɗalibai mata na manyan makarantun gaba da Sakandire na fama da yawan kai musu hari musamman ɗaliban jami'o'in arewa.

Idan baku manta ba, yan bindiga sun shiga ɗakin kwanan ɗaliban jami'ar tarayya da ke Gusau, sun sace wasu.

Kara karanta wannan

Hotunan Matasa Maza da Mata Mahaddatan Alkur'ani Sun Cika Gidan Kwankwaso Maƙil Kan Abu 1

Kwanaki kaɗan bayan haka aka sake samun labarin cewa an yi garkuwa da wasu ɗalibai mata a jami'ar tarayya da ke Dutsin-ma a jihar Katsina.

Jami'an Tsaro Sun Kashe Dan Bindiga a Kebbi

A wani rahoton kuma 'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da jami'an tsaro suka haɗu suka kai musu samame har cikin daji a jihar Kebbi.

Gwarazan dakarun da suka haɗa da sojoji, yan sanda, DSS da Sibil difens sun ceto mutane uku da aka sace, sun sheƙe ɗan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262