Kano: Attajirin Dan Kasuwa, Aminu Dantata, Ya Rasa Jikarsa Yar Shekara 40
- Babban attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata, ya shiga jimami yayin da ɗaya daga cikin matasan jikokinsa ta riga mu gidan gaskiya
- Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata ta rasu ne bayan fama da cutar sikila na taawon lokaci tana da shekaru 40 a duniya
- Wannan na zuwa ne watanni bayan Attajirin ɗan asalin jihar Kano ya rasa mai ɗakinsa, Hajiya Rabi Aminu Ɗantata a watan Afrilu
Jihar Kano - Fitaccen attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata, ya yi rashin ɗaya daga cikin jikokinsa, Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata.
Batulu ta rasu tana shekaru 40 a duniya bayan ta sha fama da jinyar ciwon sikila na tsawon lokaci, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Marigayya Batulu ta kammala karatunta na zama lauya watau Law kafin Allah ya karɓi rayuwarta. Ta rasu ta bar mahaifiyarta, Hajiya Ummul Khair Aminu Dantata.
Mahaifiyar mamaciyar ita ce ɗiya ta farko ga Alhaji Aminu Ɗantata. Haka kuma Batulu ta rasu ta bar mahaifinta, Alhaji Baba Alhassan Ahmad Dantata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a mata jana'iza?
Za a yi wa marigayya Batulu sallar jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Masallacin Jumu'a na Koki da ke cikin kwaryar birnin Kano da misalin ƙarfe 10:00 da safiyar yau Talata.
A rahoton jaridar Punch, Batulu ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Jeddah a ƙasar Saudiyya.
Idan baku manta ba, Alhaji Aminu Ɗantata, ya rasa matarsa, Hajiya Rabi, wacce Allah ya mata rasuwa a watan Afrilun wannan shekara da muke ciki 2023.
Magajin garin Zazzau ya rasu
Wannan rasuwa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jakadan Najeriya a ƙasar Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 52 a duniya.
A wata sanarwa da fadar mai martaba Sarkin Zazzau ta fitar ranar 20 ga watan Oktoba, 2023, ta ce Bamalli ya rasu ne a wani asibitin kuɗi a jihar Legas.
Maragayin shi ne magajin garin Zazzau kuma ɗan uwa na jini watau ƙani ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.
An rasa ɗai a haɗarin jirgi
A wani labarin na daban kun ji cewa akalla mutum ɗaya ne ya mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Delta.
Sai dai an samu saɓanin adadin yawan waɗanda suka mutu a haɗarin tsakanin rahoton hukumar 'yan sanda da bayanan shugaban ƙaramar hukumar da abun ya faru a yankinsa.
Asali: Legit.ng