Najeriya Ta Yi Babban Nasara Kan Kamfanin P&ID a Kotun Birtaniya

Najeriya Ta Yi Babban Nasara Kan Kamfanin P&ID a Kotun Birtaniya

  • A ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, Najeriya ta yi nasara kan kamfanin Process & Industrial Developments (P&ID) Limited a kotun Birtaniya
  • Kotun ta yi watsi da diyyar dala biliyan 11 da aka ce Najeriya ta biya P&ID, bisa hujjar cewa kwangilar siyar da gas din an kulla ta ne ta hanyar yaudara
  • Mai shari'a Robin Knowles na Kotun Kasuwanci na Ingila da Wales ne ya yanke hukuncin ta sakon imel

Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta yi nasara a shari'ar ta da kamfanin Process & Industrial Developments (P&ID) Limited a kotun Landan a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba.

Vanguard ta rahoto cewa an bada hukuncin ne bayan shafe shekara biyar ana shari'a kuma Najeriya ce ta samu nasara, yayin da kotun ta yi watsi da diyyar dala biliyan 11 da aka ce ta biya P&ID.

Kara karanta wannan

Wike: Tashin Hankali Yayin da Tsohon Kakakin APC Ya Bukaci Tinubu Da Ya Kama Sheikh Gumi

Najeriya ta yi nasara kan P&ID a kotun Birtaniya
Kotun Birtaniya ta yanke hukunci kan shari'ar Najeriya da P&ID. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, InsideBusiness.ng
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncin da aka tura da imel, Robin Knowles, Alkalin kotun Kasuwanci na Ingila da Wales, ya jadada matsayar Najeriya na cewa kwangilar gas din an bada shi na cikin yaudara, kamar yadda The Cable ya rahoto.

Hukuncin na zuwa ne bayan shugaban Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC), Gbenga Komolafe, ya bukaci wadanda suka yi nasarar samun kwangilar fara sarrafa gas din da ake asararsa don siyarwa, NGFCP, su yi gaggawa kan aikin.

Hukuncin biyan tarar dala biliyan 11: Masu amfani da intanet sun yi martani bayan nasarar Najeriya

Yan Najeriya sun yi martani a manhajar X kan hukuncin da kotun ta yanke. Legit Hausa tattaro wasu cikin martanin.

@MorrisStephn ya ce:

"Wani zai 'kashe' kudin."

@YakubuJonah5 ya rubuta:

"Maza su kawo kudin su raba wa talakawa."

@eejiofor_iz30081 cewa ya yi:

"Wannan kamfanin ya yi babban kuskure, ta sun kawo shari'ar Najeriya sai su bai wa alkalan cin hanci, har ma su iya bada takardun bogi a matsayin hujja. An gama shari'a."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sabon Yunkuri Domin Hana Amurka Fallasa Ragowar Sirrinsa a Duniya

@EseluEselu4 ta ce:

"Ina taya Najeriya murna idan da kotunmu ne na gida da sun karba rashawa sun bai wa wanda ya fi kudi nasara."

@DRREAL01 ya ce:

"Gwamnatin masu la!fi ba za su yi amfani da kudin ta hanyar da ya dace ba ...otilo."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164