Shugaba Tinubu Na Jagorantar Taron FEC Karo Na Uku a Aso Rock

Shugaba Tinubu Na Jagorantar Taron FEC Karo Na Uku a Aso Rock

  • Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) karo na uku a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
  • Wasu daga cikin ministoci da manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya ciki harda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, sun halarci zaman
  • A makon da ya shuɗe, Tinubu ya amince da canja ranar gudanar da taron FEC daga ranakun Laraba zuwa Litinin na kowane mako

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na jagorantar taron majalisar zartarwa (FEC) karo na uku kenan tun bayan kafa gwamnatinsa a fadar shugaban ƙasa.

Kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya nuna, an fara taron ne da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar rana yau Litinin, 23 ga watan Oktoba, 2023 a birnin tarayya Abuja.

Shugaba Tinubu na jagorantar taron FEC karo na uku a fadar shugaban kasa.
Shugaba Tinubu Na Jagorantar Taron FEC a Abuja Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa taron ya samu halartar mafi aƙasarin muƙarraban shugaba Tinubu, ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ƙara Yin Gyara, Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar ECN Ta Ƙasa

Haka zalika wasu daga cikin Ministocin da shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa sun samu halartar zaman FEC karo na uku a Aso Rock, Thisday ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin jiga-jigan da aka gani a taron

Waɗan da suka halarci taron sun haɗa da Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, da shugaban sashin kula da ma'aikatan tarayya, Folashade Yemi-Esan.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gabajabiamila, da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribaɗo, sun halarci zaman yau Litinin.

FG ta canja ranar taron FEC

Idan baku manta ba, Gwamnatin tarayya ta sauya ranar da za a riƙa gudanar da taron majalisar zartarwa na mako-mako daga ranar Laraba zuwa ranar Litinin.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Yi Magana Kan Wasikun da CSU Ta Bayar Kan Takardun Shugaba Tinubu

Ya kuma ƙara da bayanin cewa ba kowane mako za a riƙa gudanar da taron ba, maimakom haka za a riƙa yin taron ne idan da buƙatar hakan don magance wasu batutuwa.

Mutanen Zamfara sun aika sako ga Tinubu

A wani rahoton na daban Wasu mazauna garuruwan mazaɓar Sanatan Zamfara ta arewa sun rubuta wasiƙa zuwa ga gwamna da shugaban ƙasa Tinubu.

Mutanen a karkashin kungiyarsu, sun ja hankalin cewa 'yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankunan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262