“Ana Dole?” Wani Mutum Ya Kwanta a Kasa Don Rokon Budurwarsa, Ya Kama Kafarta
- Wani bidiyo da ke yawo ya nuno yadda wani mutum ya rirrike kafar budurwarsa yana kuka da rokonta don kada ta rabu da shi
- Yayin da mutumin ke kuka tare da mimmikewa a kasa, matar ta yi yunkurin kwace kafarta
- An jiyo mutumin yana rokon matar da kada ta bar shi dannan ya yi bayanin cewa ana horar da shi saboda so
A cikin wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, an sha yar dirama yayin da aka gano wani mutum yana jan kansa a kasa yayin da yake rokon wata budurwa wacce ga dukkan alamu sahibarsa ce don kada a rabu da shi.
Bidiyon ya nuno wani mutum kwance a kasa, hawaye na ta kwaranya daga idanunsa yayin da ya rike kafar budurwar tasa, don baya so ta kufce masa.
Cike da hawaye ya dunga rokonta kan kada ta bar shi, kalamansa suna dauke da tsantsar damuwa.
"Sikuachi (ba zan bar ki ba)," mutumin ya koka, fuskarsa duke a kasa, yana mai rike kafarta da dukka karfinsa. Ya ki janye rikon da ya yi mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mapenzi inaniuma mimi (so na aabtar da bi)," cewar shi.
A martaninta, matar ta yi kamar ta shiga rudani, tana kokarin janye kafarta domin ta fice.
"Wai dole ne?" ta tambaye shi yayin da take fafutukar yin watsi da rokon mutumin.
Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayinsu
Becky Qn:
"Wai dole ne?"
Cay KJ:
"Idan dadin abun ya cika yawa. Na fahimci yadda mutumin yake ji."
Maggie Wambui:
"Ina son irin wannan."
Pinchez Muendo:
"Mutumin nan yana bukatar horo mai tsanani, ta yaya zai kai mu kasa haka?"
Kyakkyawar baturiya ta dira Najeriya don ganin masoyinta
A wani labari na daban, masu amfani da soshiyal midiya sun mato a kan wani bidiyo da ke nuno yadda wasu masoya farar fata da bakin fata suka hadu a Najeriya.
Matashin wanda ya kasance dan Najeriya ya isa filin jirgin sama yayin da ya tarbi matashiyar budurwar da ta yi tattakin zuwa kasar.
Da yake wallafa wani bidiyo na maraba da zuwan da aka yi wa matashiyar, wani mai amfani da TikTok, @mikel_entertainer, ya rubuta:
"Sannu da zuwa Najeriya, kyakkyawan iyali."
Asali: Legit.ng