Reno Omokri Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Kamata Tinubu Ya Binciki Buhari

Reno Omokri Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Kamata Tinubu Ya Binciki Buhari

  • Jigo a jam’iyyar PDP, Reno Omokri ya bayyana cewa Buhari yana da bayanai masu yawa da zai bayar dangane da halin da ya samu Naira da kuma yadda ya bar ta
  • A cewar hadimin tsohon shugaban ƙasar, Buhari ya hau karagar mulki a talauce amma ya kwashe dukiyar ƙasar ya bar Najeriya a talauce
  • Omokri ya cigaba da cewa tsohon shugaban ƙasar ya kashe mafi yawan kuɗaɗen da ya karɓa a Jamhuriyar Nijar, inda ya yi niyyar yin ritaya amma yanzu ya maƙale a Najeriya

Reno Omokri, mai taimakawa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana yadda tattalin arzikin Najeriya ya durkushe a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Jigon a jam'iyyar PDP a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, ya yi iƙirarin cewa Buhari ya lalata kuɗin Najeriya tare da shirin tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Omokri Ya Fallasa Katobar Buhari, Ya Fadi Abin da Yan Najeriya Za Su Yi Masa da Sun San Yadda Ya Lalata Kasa

Reno Omokri ya bukaci Tinubu ya binciki Buhari
Reno Omokri ya ce ya kamata Tinubu ya binciki Buhari Hoto: Reno Omokri, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Ya yi nuni da cewa rikicin siyasar Nijar ya sa Buhari ya sauya shawara inda a ƙarshe ya yi ritaya zuwa jiharsa ta Katsina.

Omokri ya cigaba da cewa, a lokacin da Buhari ke bukatar kuɗin ƙasashen waje, ya jinginar da asusun ajiyar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa Tinubu ya kamata ya binciki Buhari, Omokri

Omokri ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya binciki Buhari da na kusa da shi kamar yadda yake binciken CBN a ƙarƙashin Godwin Emefiele.

A cewar Omokri Buhari ya hau mulki yana talaka, ya tarar da Najeriya da azriƙinta, sannan ya sauka mulki da arziƙinsa ya bar Najeriya cikin talauci.

Wani ɓangare na rubutunsa na cewa:

"Muna da ƙasa da dala biliyan 4 a asusun ajiya. Daga nan ya fara karɓar kuɗaɗen man fetur da za a siyar nan gaba a wata yarjejeniyar musaya mai cike da cece- kuce. Kusan bayan wata biyar bayan ya bar ofis, Najeriya ba ta samun kuɗi daga siyar da man fetur saboda Buhari ya karɓe kuɗaden."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jakadan Najeriya Kuma Ɗan Uwan Mai Martaba Sarkin Zazzau Ya Rasu

"Ba wai Buhari ya ci bashin da ya fi na dukkanin shugabannin ƙasar da suka gabace shi ba ne gaba ɗaya, abin ban haushi shi ne ya kashe maƙudan kuɗaɗen da ya ranta a Jamhuriyar Nijar (yana ɗaukar kansa a matsayin ɗan Nijar saboda mahaifinsa ya fito daga Nijar) da fatan zai yi ritaya a can. Amma yanzu da juyin mulkin da aka yi a Nijar, ya maƙale a Najeriya."
"Ina ministan kuɗinsa? wai ta gudu, da wata jam'iyya ce ta lashe zaɓen 2023, babu yadda za a yi Buhari ya kubuta daga gidan yari, abin da ya yi shi ne babban laifi. Ya hau mulki talaka ya tarar da Najeriya da arziƙinta, Ya fita ofis mai arziki ya bar Najeriya a talauce. Kamar yadda Tinubu ke binciken CBN, shi ma ya kamata ya binciki Buhari da na kusa da shi."

Buhari Ya Gurgunta Kasa

A wani labarin kuma, Reno Omokri ya fallasa katoɓarar da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan.

Tsohon hadimin na tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa da ƴan Najeriya sun san yadda Buhari ya gurgunta ƙasa, da sun huce fushinsu a kansa idan suka haɗu da shi a bainar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng