“Ba Zan Iya Auren Irin Wannan Ba”: Bidiyon Matashi Yana Gulma a Gidan Kitso Ya Ba Mata Mamaki

“Ba Zan Iya Auren Irin Wannan Ba”: Bidiyon Matashi Yana Gulma a Gidan Kitso Ya Ba Mata Mamaki

  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wani matashi da ke gulma cikin salo a shagon gyaran gashi
  • Matashin na gulma cike da kwarewa, yana jujjuya jikinsa cikin yanayi mai ban dariya domin ganin jawabinsa ya isa ga abokin tseguminsa
  • A ganin farko, wasu mutane sun zata yana da wata tawaya ne a jikinsa, yayin da yadda yake yi da jikinsa ya ba wasu dariya

Wani matashi ya yi fice bayan wani bidiyonsa yana gulma a shagon gyaran gashi ya yadu a soshiyal midiya.

Wani abokin mutumin ya wallafa bidiyon a TikTok dauke da taken, 'POV: Idan abokinka na son gulma...gani ya kori ji.'

Wani mutum yana jujjuya jikinsa yayin da yake gulma
“Ba Zan Iya Auren Irin Wannan Ba”: Bidiyon Matashi Yana Gulma a Gidan Kitso Ya Ba Mata Mamaki Hoto: @demionbeautyworld
Asali: TikTok

Yayin da ba'a bayyana abun da suke tsgumin a kai ba a bidiyon, mutumin ya mayar da hankali sosai wajen isar da sakonsa ga wani a gefe.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Abin Da Cire Takunkumin CBN Yake Nufi Ga Manoma Da Abinci, Masani

Ya yi magana cikin sigar da yasa mutane da dama son sanin abun da yake fada ma sauran mutane. Yadda yake jujjuya jikinsa da farko ya bai wasu mutane tsoro, sannan wasu da dama sun dara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alamu sun nuna wanda ya wallafa bidiyon, @demionbeautyworld, shine ya dauki bidiyon da kansa a gidan gyaran gashin.

Jama'a sun yi martani kan bidiyon

iam_praize ya ce:

"Ko mutumin da ke karya zuciya bai taba kalmasa wuyansa kamar haka ba."

Becky ta ce:

"Ba zan iya auren irin wannan mutumin ba faaaa....sirrina zai kare a waje."

Humxks ta ce:

"Lol, mutane masu yin irin haka da jikinsu sune nake son samun labarina daga wajensu. Saboda basu taba ba da rabin labarin."

Ihilosen ya ce:

"Wani irin hira ne wannan yake sanya shi juya wuyansa haka."

Princess lily ta ce:

Kara karanta wannan

"Ga Kyau, Ga Kuruciya”: Dan Najeriya Ya Tarbi Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya a Filin Jirgin Sama, Bidiyo

"Har na kusa gama rubuta Allah ya baka lafiya."

ritamicheal50 ta ce:

"Da farko na zata yana fama da shanyewar barin jiki ne."

Vera ta ce:

"Da farko na zata farfadiya ce ke damunsa."

Uwar gulma ta haura kofar gida don kai ghulma ga kawarta a gidan haya

A wani labarin, wata budurwa ta ba da mamaki yayin da ta tsallaka katanga don kai gulma ka kawarta.

An yada faifan bidiyon inda budurwar ke tsallake kofar shiga gidan duk da wayoyin da ke kai kawai don gulma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng