Gobara Ta Tashi A Matatan Man Najeriya Da Ke Warri, In Ji NNPC
- An samu tashin wani karamin gobara a kamfanin tace man fetur na NNPC da ke garin Warri na Jihar Delta a ranar Juma'a
- Kamfanin na NNPC ne ya sanar da hakan yana mai cewa aikin walda da aka gudanarwa a husumiyar sanyaya abubuwa ne ya janyo karamin gobarar
- Tuni dai jami'an tsaro da ke aiki a kamfanin na NNPC da ke Warri suka shawo kan gobarar kuma kamfanin ya ce hakan ba zai kawo tsaiko ga aikin gyara da ake yi ba
Warri, Jihar Delta - Kamfanin Tace Man Fetur na Najeriya, NNPC ya ce an samo tashin karamin gobara a matatanta da ke Warri.
A cikin wata sanarwa da NNPC ta fitar a ranar Juma'a, mahukunta kamfanin sunce abin ya faru a yau, a sashin sanyaya matatan, rahoton The Cable.
Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPC ta bayyana sanadin gobarar
NNPC aikin walda da ake yi a saman husumiyan sanyaya matatan ne ya janyo gobarar.
Sai dai, kamfanin ta yi karin bayani cewa gobarar ba zai shafi aikin gyare-gyare da aka shirya yi ba.
Sanarwar ta ce:
"A yinun yau, misalin karfe 3.02, an samu karamin gobara a husumiyar sanyaya danyen mai na Matatan Mai na Warri, WRPC.
"Gobarar da ya faru sakamakon aikin walda da ake yi a saman husumiyar sanyaya mai ba zai shafi gyara da aka shirya yi ba."
A cewar sanarwar, Kamfanin NNPC ta ce jami'an tsaro da ke matatan sunyi gagawan kashe gobarar misalin karfe 3.30."
Gobarar ba zai shafi aikin gyaran mu ba - NNPC
NNPC ta ce tuni an cigaba da ayyuka kamar yadda aka saba.
Kamfanin ya ce zai cigaba da bin dukkan ka'idojin tsare lafiya a dukkan ayyukansa.
Heineken Lokpobiri, karamin ministan albarkatun man fetur ya ce matatan na Warri zai fara aiki a karshen watanni hudu na 2024.
Ya ce matatan na Fatakwal zai fara aiki karshen shekara yayin da matatan Kaduna zai fara aiki kusan karshen shekara mai zuwa.
Bola Tinubu: Za a Sayar Da Wasu Kamfanonin Gwamnati Domin Samun Kudade
A wani rahoton, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara tunanin sayar da kasonta da ke cikin kamfanoni kimanin 20, za a yi hakan ne don samun kudin shiga.
Rahoto ya fito daga Bloomberg, a ranar Talata cewa NNPC ya na cikin kamfanonin da Gwamnatin Tarayya ta ke tunanin sayar da hannun jarinta.
Asali: Legit.ng