Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi Magajin Zazzau
- Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, ambasadan Najeriya a Morocco ya kwanta dama kamar yadda rahotanni suka tabbatar yau Jumu'a
- Marigayin shi ne Magajin garin Zazzau, kuma ya rasu ne yayin da yake hanyar zuwa Arewacin Afirka
- Akwai wasu muhimman abubuwa game da Basaraken wanda ya dace a ce kun san su, mun tattara muku su a wannan shafin
A yau Jumu'a, 20 ga watan Oktoba, 2023 aka wayi gari da labarin rasuwar Magajin Garin Zazzau, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli.
Marigayi jakadan Najeriya na ƙasar Morocco ya riga mu gidan gaskiya a jihar Legas yayin da yake kan hanyar zuwa mahallinsa da ke Arewacin Afirka.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Mansur Nuhu Bamalli, ya rasu ne yana da shekara 42 a duniya kuma ya bar mata ɗaya da 'ya'ya guda biyu.
A wannan shafin, mun tattara muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata a ce kun sani game da mamacin, ga su kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙanin mai martaba Sarkin Zazzau
Marigayi Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, ya kasance ɗan uwa kuma ƙanin mai martaba Sarkin Zazzau a jihar Kaduna, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.
Sarauta
Kafin rasuwarsa, Alhaji Mansur shi ke riƙe da sarautar Magajin Garin Zazzau da ke Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Aikin gwamnati
Tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe karƙashin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta naɗa Mansur Bamalli a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Morocco.
Kafin Buhari ya naɗa shi wannan muƙami, marigayin shi ne mataimakin Darakta a ma'aikatar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Zuri'arsa
Mahaifinsa Nuhu Bamalli shi ne shugaban karamar hukumar Kaduna kuma Magajin Garin Zazzau, wanda ya kasance babban marubuci.
Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1
Shi ya ƙirkiro da Hawan Sallah na gargajiya a Kaduna tsawon shekaru da ya yi a wannan matsayi.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Bode Agusto, tsohon DG na ofishin kasafin kuɗin tarayya ta rasu
A wani rahoton kuma kun ji cewa tsohon darakta janar na ofishin kasafin kuɗi a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 68 a duniya.
Marigayi Mista Agusto, shi ne wanda ya kafa kamfanin Agusto & Co., hukumar kididdiga ta farko ta Najeriya.
Asali: Legit.ng