“Ina Alfahari, Farin Ciki Da Gamsuwa Cewa Na Iya Girki”, In Ii Wike

“Ina Alfahari, Farin Ciki Da Gamsuwa Cewa Na Iya Girki”, In Ii Wike

  • Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana abun da yake matukar son yi da lokacinsa baya ga aikin kasa
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa yana son yin girki kuma baya kunyar yin haka
  • Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai kuma matsayinsa ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu a soshiyal midiya

Ministan babban birnin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada cewa yana matukar alfahari da kwarewarsa a bangaren girki.

Wike ya ce yana alfahari da iya girki
“Ina Alfahari, Farin Ciki Da Gamsuwa Cewa Na Iya Girki”, Inji Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Me yasa nake son girki? Wike ya yi bayani

Da yake magana kan kwarewarsa a girki yayin wata hira da manema labarai a ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, Wike ya ce girki na cin lokacinsa da janye hankalinsa daga siyasa.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 Da Sheikh Gumi Ya Fadi a Sabon Bidiyonsa Da Suka Tayar Da Kura

"Ina alfahari cewa na iya girki, kuma ina farin ciki a duk sanda na ci shi. Na gamsu."

Ku tuna cewa Wike ya ja hankali a wani bidiyo da ya yadu yan kwanaki da suka gabata bayan an nuno shi yana girka abinci a kicin yayin da ya karbi bakuncin Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran baki a gidansa da ke Abuja.

Da yake martani ga ci gaban, Wike, ya bayyana ra'ayinsa kan lamarin, yana mai cewa yadda aka tayar da shi yasa ya daurawa kansa nauyin shiga kicin, rahoton Channels TV.

Ministan ya bayyana cewa yayin da wasu mutane ke kallon girki a matsayin bata lokaci, shi yana jin dadin girki kuma yana gamsuwa.

Kalli bidiyon a kasa:

Wike ya ba da wa’adin sa’o’i 24 ga hukumar FCDA don samo tsarin biyan diyyar masallacin Abuja

A wani labari na daban, mun ji cewa minsitan Abuja, Nyesom Wike ya bai wa sakataren hukumar FCDA wa’adin sa’o’i 24 don yin bayanai kan matsayar babban masallacin Abuja.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Zazzafan Martani Yayin da Sheikh Gumi Ya Kira Wike Da "Shaidanin Mutum"

Wike ya bukaci hakan ne daga sakataren, Injiniya Shehu Ahmed don sanin wurin da masallacin ya ke da kuma tsarin kudin diyya da za a biya.

Hausa Legit ta tattaro cewa aikin fadada hanya a yankin zai shafi wani bangaren babban masallacin da ke birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng