Tinubu Ya Sallami Shugabannin NBC, NAN Da NTA, Ya Nada Sabbi
- Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a Ma’aikatar Yada Labarai da Hukumar Wayar da Kan Jama’a
- Tinubu ya yi sabbin nade-naden ne har guda takwas wadanda za su yi aiki karkashin ma’aikatar Yada Labarai
- Hadimin shugaban a bangaren kafar sadarwa ta zamani, David Olusegun shi ya bayyana haka a yau Alhamis ashafin Twitter
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sabbin nade-nade a Ma’aikatar Yada Labarai da Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA).
Tinubu ya nada Mista Lanre Issa Onilu a matsayin shugaban Hukumar ta NOA yayin da ya nada Salihu Abdulhamid Dembos shugaban Gidan Talabijin na Kasa, NTA.
Su waye Tinubu ya nada a hukumomin?
Hadimin shugaban a bangaren kafar sadarwa ta zamani, David Olusegun shi ya tabbatar da haka a shafinsa a Twitter a yau Alhamis 19 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya nada mutane takwas a hukumomin wanda za su yi aiki karkashin ma’akatar Yada Labarai.
Sanarwar ta ce:
"Shugaba Tinubu ya nada sabbin shugabanni a ma'aikatar yada labarai ta kasa."
Legit Hausa ta jero muku jerin sabbin nade-naden:
1. Mista Lanre Issa Onilu - shugaban hukumar NOA
2. Mista Salihu Abdulhamid Dembos - shugaban NTA
3. Dakta Mohammed Bulama - shugaban hukumar FRCN
4. Mista Charles Ebuebu - shugaban hukumar NBC
5. Jibrin Baba Ndace - shugaban hukumar VON
6. Dakta Lekan Fadolapo - shugaban hukumar ARCON
7. Ali Mohammed Ali - shugaban hukumar NAN
8. Mista Dili Ezughan - shugaban hukumar NPC."
Wane gargadi Tinubu ya yi ga sabbin nade-naden?
Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin da su yi aiki don kawo sauyi a hukumominsu daban-daban, Legit ta tattaro.
Tinubu ya kuma bukace su da su yi iya yinsu don ganin sun hada kan 'yan kasar da sauya tunanin mutane da kuma daga martabar kasar a idon duniya.
Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar ICPC, Dakta Adamu Aliyu Musa a ranar Talata 17 ga watan Oktoba.
Majalisa ta tabbatar da nadin shugaban EFCC, NSIPA
A wani labarin, majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin shugaban hukumar EFCC da NSIPA a jiya Laraba.
Majalisar ta amince da nadin Ola Olukoyede da Halima Shehu a matsayin shugabannin hukumomin.
Har ila yau, majalisar ta kuma tabbatar da mukamin sakataren Hukumar EFCC, Mohammed Hammajoda.
Asali: Legit.ng