Tsohon DG Na Ofishin Kasafin Kuɗin Najeriya, Bode Agusto, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Bode Agusto, tsohon DG na ofishin kasafin kuɗin tarayya ta rasu yana da shekaru 68 a duniya
- Mista Olufemi Awoyemi, Shugaba kuma mamallakin kamfanin Proshare Nigeria ne ya sanar da rasuwar ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, 2023
- Ya bayyana cewa ba zai taɓa manta wa da shi ba saboda rawar da ya taka wajen koya musu darasin rayuwa da mutunta gaskiya komai ɗacinta
FCT Abuja - Tsohon Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya kuma masanin tattalin arziki, Bode Agusto, ya riga mu gidan gaskiya.
An tattaro cewa tsohon DG ɗin ya mutu ne yana shekaru 68 a duniya ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, 2023.
Marigayi Mista Agusto, shi ne wanda ya kafa kamfanin Agusto & Co., hukumar kididdiga ta farko ta Najeriya.
Shugaba kuma wanda ya kafa kamfanin Proshare Nigeria, Mista Olufemi Awoyemi, ne ya sanar da labarin rasuwar Agusto a ranar Alhamis, a shafinsa na manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da ya wallafa, Mista Awoyemi ya ce:
"Bode Agusto (@bodeagusto) wanda ya kafa @agustoandco, shi ne jagaba wanda ya koya mana dukkan yadda ake mutunta gaskiya da bayanai a cikin ayyukan mu."
“Babban mutum ne kuma ƙwararren malami, darussan da ka koya mana, wanda suka shiga al'amuran mu, ba za su taɓa gushewa daga gare mu ba. Nasarorin da muka samu duk silarka ne."
"Ina rokon Allah madaukakin Sarki da ya ba 'yan uwansa da dangi karfin gwiwar tsallake wannan laokaci na babban rashin da suka yi. Ina kuma roƙon Allah ya sa ya samu salama."
Taƙaitaccen tarihinsa
Mamacin ya samu shaidar kammala digirin farko a fannin lissafin kudi (Accounting) a Jami’ar jihar Legas daga shekarar 1974 zuwa 1977.
Badakalar Kwangila: Shugaban EFCC Ya Tona Asiri Kan Asarar da Najeria Ta Yi Cikin Shekaru 3 Na Buhari
Haka nan kuma ya zama cikakken mamban Cibiyar Institute Of Chartered Accountants of Nigeria a shekarar 1981.
Hukumar PSC Ta Kare Kanta Kan Daukar Tubabbun 'Yan Daba Aiki a Jihar Kano
A wani rahoton kuma Hukumar jin daɗin 'yan sanda ta ƙasa (PSC) ta kare matakin ɗaukar tubabbun 'yan daba aikin kurtu a jihar Kano
Kakakin PSC na ƙasa, Ikechukwu Ani, ya ce 'yan daban da suka tuba aka ɗauke su aikin sun gane aikata laifi ba ya haifar da ɗa mai ido
Asali: Legit.ng