Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 6 a Wata Kasuwa a Jihar Cross Rivers
- Wata mummunar gobara da ta tashi a wata fitacciyar kasuwa a birnin Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa
- Gobarar wacce ta tashi a kasuwar Watt ta laƙume kayan miliyoyin nairori a wasu shaguna guda shida da ta kama
- Jami'an hukumar kashe gobara sun kawo agajin gaggawa inda suka samu nasarar daƙile gobarar yaɗuwa zuwa sauran shaguna a kasuwar
Calabar, jihar Cross Rivers - An yi asarar kayayyaki na miliyoyin nairori bayan wata mummunan gobara ta tashi a kasuwar Watt da ke birnin Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa gobarar ta tashi ne da safiyar ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoban 2023, inda ta lalata dukiya mai tarin yawa.
Gobarar wacce aka ce ta tashi ne da misalin ƙarfe biyu na safe, ta ƙone aƙalla shaguna shida a cikin rukunin shagunan da gobarar ta tashi.
Menene ya haddasa tashin gobarar a kasuwar?
Kwamandan hukumar kashe gobara ta shiyyar Calabar, Mrs Olumayowa Olomola, wacce ta tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin, ta ce gobarar ta tashi ne a dalilin tartsatsin wuta a ɗaya daga cikin manyan kantunan kasuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olomola, wacce ba ta bayyana ƙiyasin kayayyakin da aka lalata a shagunan da abin ya shafa ba, ta ce shagunan cike suke maƙil da kayayyaki, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Ta ce amma saboda ceton da jami'an hukumar suka kawo cikin gaggawa, an samu nasarar daƙile gobarar ba ta shafi sauran shagunan ba.
Olomola ta bayyana cewa:
"Ɗaukin da muka kawo a kan lokaci ya sanya muka iya dakatar da gobarar a iya shagunan guda shida da abun ya shafa."
"Shawarata ita ce a koda yaushe mu ɗauki matakan kariya ta hanyar tabbatar da cewa mun kashe dukkan na'urori domin guje wa aukuwar irin hakan."
Gobara Ta Tashi a Ma'ajiyar Man Fetur
A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta tashi a wata ma'ajiyar adana man fetur a Seme-Krake a Jamhuriyar Benin.
Gobarar wacce aƙalla mutum 35 ne suka ƙone ƙurmus a dalilinta, ta tashi ne yayin da ake sauke man fetur ɗin da aka yi fasaƙwaurinsa daga Najeriya a cikin ma'ajiyar.
Asali: Legit.ng